Gwamnoni Sun Kafa Sharadi ga Tinubu kan Kudirin Haraji

Gwamnoni Sun Kafa Sharadi ga Tinubu kan Kudirin Haraji

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya sake magana kan kudirin haraji da ya jawo ce-ce-ku-ce tsakaninsu da Bola Tinubu
  • Abdullahi Sule ya ce gwamnonin Arewa ba su yin adawa da sauya fasalin haraji a Najeriya kawai suna bukatar a yi gyara ne
  • Gwamnan ya ce shi gogaggen ma'aikaci ne da ya jagoranci ma'aikata da ke biyan haraji saboda haka ya ke so a gyara kudirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Gwamnan Nasarawa ya yi karin haske kan kudirin haraji da Bola Tinubu ya gabatar a majalisa.

Abdullahi Sule ya ce a hakikanin zance gwamnonin Arewa ba adawa suke yi da kudirin ba kawai gyara suke so a yi.

Abdullahi Sule
Gwamnan Nasarawa ya fadi yadda za su shirya da Tinubu kan haraji. Hoto: Abdullahi Sule|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya yi bayani ne a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Lafia.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda gwamnati ta tunkari matsalar tattalin arziki gaba gadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni sun kafawa Tinubu sharadi

Gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana cewa har yanzu suna kan bakarsu ta kin amincewa da kudirin haraji na Bola Ahmed Tinubu.

Abdullahi Sule ya bayyana cewa suna bukata shugaba Bola Tinubu ya yi sauyi ga kudirin kafin su amince da shi.

The Nation ta wallafa cewa gwamnan ya ce akwai bukatar sake nazarin harajin VAT wanda kuma dama a kansa ne aka samu takaddama tsakaninsu da Tinubu.

"Ba adawa muke da sauya fasalin haraji na Bola Tinubu baki daya ba, akwai abubuwa masu fa'ida a cikinsa.
Muna bukatar a sake dubi kan maganar tattara harajin VAT ne. Muna so a cire harajin VAT a cikin kudirin."

- Gwamna Abdullahi Sule

A yanzu haka kallo ya koma kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin ganin ko zai saurari bukatar gwamnonin.

An kashe masu karbar haraji

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Delta na nuni da cewa wasu masu karban haraji sun hadu da ajalinsu a cikin wata kasuwa.

Kara karanta wannan

"Lakurawa sun zo da shiri:" Bukarti ya ce yan ta'adda sun yi shekaru a Najeriya

Lamarin ya faru ne biyo bayan takun saƙa da ake samu tsakanin kabilu guda biyu a kan wanda yake da ikon karɓar haraji a cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng