Ana Murna Gwamna a Arewa Ya Amince da Sabon Albashi, Ya Fadi Lokacin Fara Biya

Ana Murna Gwamna a Arewa Ya Amince da Sabon Albashi, Ya Fadi Lokacin Fara Biya

  • Gwamnatin jihar Plateau ta sanar da sabon mafi ƙarancin albashin da za ta riƙa biyan ma'aikata duk wata
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya amince a fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashin N70,000
  • Shugaban ma'aikatan gwamnati ya ce an yi hakan ne domin inganta walwala da jin daɗin ma'aikatan Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan Plateau, Barista Caleb Mutfwang ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamna Caleb Mutfwang ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar nan take.

Mutfwang ya amince da sabon albashi a Plateau
Gwamna Mutfwang ya amince da sabon mafi karancin albashi Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan jihar, Stephen Gadong, ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Plateau ya amince da sabon albashi

Amincewar ta biyo bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da kwamitin da aka kafa ya yi kan ƙarin albashin a ranar Laraba 13 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Ma'aikata na murna da kudi mai tsoka, Gwamna ya dakatar da biyan sabon albashi

Stephen Gadong ya bayyana cewa aiwatar da sabon albashin ya nuna ƙudirin gwamnati na ba da fifiko kan jin daɗin ma’aikatanta, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Ya ce gwamnatin ta kuma aminta da gagarumar rawar da ma'aikatan suke takawa wajen cimma manufofin ci gaba na gwamnati.

Stephen Gadong ya buƙaci ma’aikatan gwamnatin da su rungumi wannan karimcin da aka yi musu ta hanyar sake jajircewa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ma'aikata za su samu sauƙi

Ziya'ulhaq Dauda Adamu ya shaidawa Legit Hausa cewa ma'aikata za su samu sauƙi idan aka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin.

Ya bayyana cewa yadda rayuwa ta yi tsada a yanzu, duk wani ƙari da za a samu zai taimaki ma'aikata.

"Eh tabbas ma'aikata za su samu sauƙi idan aka fara biyan sabon albashin. Fatanmu dai shi ne Allah ya sa ka da a ɗauki dogon lokaci wajen fara biya."

- Ziya'ulhaq Dauda Adamu

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Zamfara ta fadi lokacin fara biyan N70,000

Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Zamfara zai biya albashin N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Zamfara ta yi magana kan lokacin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.

Gwamnatin ta hannun shugaban ma'aikatan jihar, Ahmad Liman, ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara biyan akalla N70,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng