An Soki Matar Tsohon Gwamna da Ta Kira Najeriya Gidan Dabbobi, An Zagi Mijinta a Kabari

An Soki Matar Tsohon Gwamna da Ta Kira Najeriya Gidan Dabbobi, An Zagi Mijinta a Kabari

  • Matar marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta jawo kanta zagi da kuma mijinta da ke cikin kabari
  • Ana zargin Betty Akeredolu ta yi rubutu a shafin X inda ta kira Najeriya da gidan 'zoo' da bai yi wa yan kasar dadi ba
  • Betty tana magana ne bayan ta kwatanta zaben shugaban kasar Najeriya da aka yi a 2023 da na Amurka da aka gudanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Ana shirin gudanar da zaben jihar Ondo, matar tsohon gwamna, marigayi Rotimi Akeredolu ta tayar da kura.

Betty Akeredolu ta yi rubutu a kafar sadarwa wanda yan Najeriya suka caccake ta a kai saboda rashin dacewa.

Matar tsohon gwamna ta shiga matsala da ta kwatanta Najeriya da gidan 'zoo'
Matar marigayi tsohon gwamnan Ondo ta jawowa kanta zagi a kafafen sadarwa. Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi.
Asali: Facebook

Matar tsohon gwamna ta soki zaben Najeriya

Betty Akeredolu ta yi magana a shafin X, ta kwatanta Najeriya da gidan 'zoo' bayan wani ya yi mata martani kan maganarta.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Jerin gwamnoni da suka mulki jihar daga 1999 zuwa yanzu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce, wasu suka ce tana daga cikin wadanda suka mori gwamnatin zalunci.

"Ina tuna zaben shugaban kasar Najeriya a 2023 mai kuri'u miliyan 25 amma an shafe kwanaki biyar ana kirge."
"Zaben shugaban kasar Amurka a 2024 mai kuri'u miliyan 155, an kammala kirge a cikin awanni 10."

- Betty Akeredolu

Wani mai amfani da kafar X ya yi mata martani, ya ce ce gaskiya daci ne da ita.

Betty ta yi masa martani da cewa:

"Tabbas gaskiya daci gare ta, waye zai ceto Najeriya kasa kamar gidan 'zoo'."

Wannan martani nata bai yiwa yan Najeriya da dama dadi ba inda suka caccake ta.

Martanin wasu yan Najeriya ga Betty Akeredolu

@sankofa360:

"Saboda kalubale a kasa ba zai mayar da ita gidan 'zoo' ba, musamman kasar ta mayar da ke yadda kike a yanzu."

@kingkhone4real:

"Ki na zubarwa kanki mutunci ne da kuma marigayi mijinki saboda kun ci ribar lalacewar kasar da kuma ba da gudunmawa."

Kara karanta wannan

'Babu mai karya ni': Wike ya fusata kan rigimar PDP, ya soki gwamna kan matsalarta

@YeyeOba001:

"Tabbas da a ce Akeredolu zai dawo duniya cikin hankalinsa ba zai sake zama da ke ba."

Lẹykìí@Olalekanakogun:

"Gidan 'zoo'? kasar kenan da mijinki ya yi shugabancin NBA da kuma zama gwamna na kusan tsawon shekaru takwas."

Betty ta ƙaryata zancen auren kanin Akeredolu

Kun ji cewa an yada jita-jitar cewa Betty Akeredolu, matar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta auri kaninsa bayan rasuwarsa.

A wani shafin X ya wallafa cewa Betty za ta sake auren ne a ranar 6 ga watan Afrilun 2024 inda aka gano ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.