Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin Zamfara Ta Fadi Lokacin Fara Biyan N70,000

Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin Zamfara Ta Fadi Lokacin Fara Biyan N70,000

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana shirinta na fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 duk wata
  • Shugaban ma'aikatan gwamnatin Zamfara ya ce nan ba da jimawa ba Gwamna Dauda Lawal zai fara biyan sabon albashin
  • Ahmad Liman ya ce ana jiran rahoton kwamitocin da aka ɗorawa alhaki kan mafi ƙarancin albashin ne kafin fara aiwatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta yi magana kan lokacin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.

Gwamnatin ta hannun shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Ahmad Liman, ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamnatin Zamfara za ta biya mafi karancin albashi
Gwamnatin Zamfara za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Alhaji Ahmad Liman ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a Gusau a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya kinkimo aikin da zai laƙume Naira biliyan 20

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ma'aikatan ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na inganta jin daɗin ma’aikatan jihar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Gwamnan Zamfara zai biya N70,000

Alhaji Ahmad Liman ya bayyana cewa tuni Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar.

"Kun san gwamnatin jiha ta kafa kwamitin tantance ma’aikatan gwamnati da na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000."
"Kwamitocin biyu suna yin aiki ba dare ba rana domin kammala aikin da aka ba su."
"Ana sa ran kwamitocin biyu da ke gudanar da aikin za su kammala aikinsu a ƙarshen wannan wata na Nuwamba."

- Alhaji Ahmad Liman

Alhaji Ahmad Liman ya ce da zarar kwamitocin sun kammala aikinsu tare da gabatar da rahotonsu ga gwamna, zai amince da sabon mafi ƙarancin albashin ga ma'aikatan jihar.

Gwamnan Taraba ya amince da sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai girma gwamnan Taraba Agbu Kefas ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar NLC, gwamna a Arewa ya amince da sabon mafi karancin albashi

Gwamna Agbu Kefas ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati a jihar Taraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng