Zargin da Shugaban NNPP Ya Yi wa Sanata Kawu har ake Barazanar Kai Shi Kotu
- Rikicin jam'iyyar NNPP ya na kara kamari a lokacin da shugabancin jam'iyyar da Sanata Kawu Sumaila ke musayar yawu
- A baya bayan nan aka ji Sanata Kawu Sumaila ya bukaci shugaban jam'iyyarsa, Dr. Hashimu Dungurawa ya ba shi hakuri
- Sanata Kawu Sumaila ya ce matukar Dungurawa bai janye kalaman da ya yi a kansa ba, zai maka shi gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rikicin cikin gida da ke kokarin daidaita NNPP reshen jihar Kano ya dauki wani salo bayan Sanata Kawu Sumaila ya gargadi shugaban jam'iyyar, Hashimu Dungurawa.
Sanata Kawu Sumaila ya fusata ne bisa zargin Dr. Hashim Dungurawa ya yi masa na yarfen siyasa da wasu zarge- zarge.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Hashimu Dungurawa ya musanta cewa Sanatan ya ja kunnensa ko aika masa da wasika kan batun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin shugaban NNPP da ya fusata Sanata
Jaridar Punch ta tattaro cewa Sanata Kawu Sumaila ya na zargin Hashimu Dungurawa da karyar cewa ya karkatar da kudin al'umarsa a majalisa.
Haka kuma a cewar Kawu Sumaila, shugaban NNPP ya zarge shi da karbar $80m daga wani dan majalisar wakilai, Abubakar Kabiru Bichi domin tabbatar da APC ta yi nasara a zaben 2023.
Shugaban NNPP ya musanta karbar wasikar Sanata
Shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa ya ce babu wanda ya ba shi wata wasikar jan kunne kan kalaman da Kawu Sumaila ke zargin ya furta.
“ Ban karbi wata wasika ba, kuma babu wata wasika da aka rubuta gare ni a kan batun. Wannan ba komai ba ne face ayyukan makiya masu yada jita-jita," inji Dungurawa.
Sanata ya yi barazana ga shugaban NNPP
A baya mun ruwaito cewa Sanata Kawu Sumaila ya yi barazanar maka shugaban jam'iyyarsa ta NNPP a gaban kotu bisa zargin yi masa kage a lokacin da dambarwarsu ke kara kamar.
Sanata Kawu Sumaila ya mika barazanar ta hannun lauyoyinsa, inda ya ce ba zai zauna ya yi kurum ana yi masa kage ba, ya nemi Dakta Hashimu Dungurawa ya gaggauta ba shi hakuri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng