Sojoji Sun Saki Wuta ta Sama da Kasa kan Lakurawa, Miyagu Sun Fara Gudu

Sojoji Sun Saki Wuta ta Sama da Kasa kan Lakurawa, Miyagu Sun Fara Gudu

  • Rundunar sojin Najeriya ta ragargaji yan ta'addar Lakurawa da suka ɓulla a Arewa maso Yammacin Najeriya inda lamarin ya kai suka fara gudu
  • Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin ta kara tura jami'ai jihar Kebbi yayin da miyagun suka kashe mutane da dama a wani hari da suka kai
  • Gwamnatin Kebbi ta bayyana matakan da za ta cigaba da dauka domin tabbatar da kare dukiya da lafiyar al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Hukumomi a jihar Kebbi sun fitar da sanarwa kan wuta da aka fara saki a kan yan ta'addar Lakurawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yanzu haka an fara samun nasara kan miyagu Lakurawa a jihar Kebbi.

Sojoji
Sojoji sun ragargaji Lakurawa. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sojoji sun kwato wasu kayyakki daga hannun yan ta'addar yayin da suka tsere.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun ji ruwan alburusai, sun fara guduwa daga Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An saki wuta kan Lakurawa a Kebbi

Rundunar sojin Najeriya ta kai zafafan hare hare kan Lakurawa da suka fara ta'addanci a Arewa ta Yamma.

Leadership ta wallafa cewa miyagun sun fara guduwa a jihar Kebbi yayin da sojojin Najeriya suka musu ruwan wuta ta sama da kasa.

Dama dai gwamnatin jihar Kebbi ta nemi agajin hafsun tsaron Najeriya yayin da Lakurawa suka kai wani hari a Mera.

An kwato shanu a wajen Lakurawa

Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa bayan sakin wuta kan miyagun, sun tsere sun bar wasu kayayyaki.

Daga cikin abubuwan da aka kwato a wajen Lakurawa akwai shanu da dama da suka sace wajen al'umma.

Managar gwamnatin jihar Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alkawarin cigaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyar al'umma.

A yan kwanakin nan labarin Lakurawa ya cika kafofin sada zumunta bayan ɓullarsu a jihohin Sokoto da Kebbi.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun fara firgita jama'a, gwamnatin Tinubu ta fadi matakan da ta dauka

Ribadu ya yi magana kan Lakurawa

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya ja kunnen ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa.

Nuhu Ribadu ya gargaɗi ƴan ta'addan da cewa sun zo a lokacin da ba za su kai labari ba domin shugaban kasa Bola Tinubu ne a kan mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng