'A Watsar da Kundin Mulkin 1999': An Bayyana Yadda Za a Magance Matsalolin Najeriya

'A Watsar da Kundin Mulkin 1999': An Bayyana Yadda Za a Magance Matsalolin Najeriya

  • Emeka Anyaoku ya bayyana cewa zai yi wuya Najeriya ta warware matsalolinta idan ba ta watsar da kundin mulkin 1999 ba
  • Ya jaddada cewa Najeriya na bukatar tsarin tarayya na hakika, wanda zai kawo zaman lafiya da ci gaban al'ummomin kasar
  • Anyaoku ya yaba wa Farfesa Akinjide Osuntokun, yana tuna yadda ya taimaka masa ya zama shugaban kungiyar Commonwealth

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Tsohon shugaban Commonwealth, Cif Emeka Anyaoku, ya ce ba za a iya magance matsalolin Najeriya ba har sai an watsar da kundin tsarin mulki na 1999.

Cif Anyaoku ya jaddada cewa Najeriya, na bukatar tsarin tarayya na hakika domin magance bambance0bambancen mutanenta da kuma kawo zaman lafiya.

Cif Emeka Anyaoku ya yi magana kan amfani da kundin tsarin mulkin Najeriya na 199.
Cif Emeka Anyaoku ya nemi a daina amfani da kundin tsarin mulki na 1999 a Najeriya. Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

"A watsar da kundin mulkin 1999" - Anyaoku

Cif Anyaoku ya soki masu zagin shugabannni kan matsalolin kasar, yana mai cewa babu wani shugaba da zai iya gyara kasar sai an canja tsarin mulki, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Babu mai karya ni': Wike ya fusata kan rigimar PDP, ya soki gwamna kan matsalarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wannan maganar ne a wajen kaddamar da littafin tarihin Farfesa Akinjide Osuntokun a Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa da ke Legas.

Anyaoku ya nuna cewa Najeriya tana da al'umma, addinai, harsuna da al'adu daban daban, don haka akwai bukatar tsarin da zai girmama wadannan bambancin.

Hanyar magance matsalolin Najeriya

Tsohon shugaban na Commonwealth ya kwatanta Najeriya da Indiya, Kanada da Switzerland, wadanda suka yi nasara ta hanyar amfani da tsarin mulkin tarayya na hakika.

Anyaoku ya jaddada cewa dole ne Najeriya ta watsar da kundin mulkin 1999 tare da komawa tsarin tarayya na hakika domin warware matsalolinta.

Ya yaba wa Farfesa Akinjide Osuntokun a matsayin masani kuma mai kishin kasa, yana tuna gudunmawar da ya ba shi lokacin da yake neman shugabancin Commonwealth.

Tinubu zai karbi kudurin sauya tsarin mulki

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu zai karbi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya zuwa 'gwamnatocin shiyya na Firimiya.'

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya tona asirin yan Majalisar Tarayya, ya fadi faman da ya yi da su a INEC

Idan har shugaban kasar ya sa hannu kan wannan kudiri, shiyyoyin Najeriya za su zama karkashin 'Firimiya' kamar yadda aka yi kafin juyin mulkin soja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.