Dan Majalisar Kano Ya Jawo Surutu, An Hango Shi da Kudi Cike da Daki Ana Matsin Rayuwa

Dan Majalisar Kano Ya Jawo Surutu, An Hango Shi da Kudi Cike da Daki Ana Matsin Rayuwa

  • Dan majalisar wakilai daga Kano, Aliyu Sani Madakin Gini ya jawo abin magana bayan an samu wanio bidiyonsa da tarin kudi
  • An gano Hon. Aliyu Sani Madakin Gini da damin Naira, daurin dubu-dubu ana kirga su a wani wuri da ya yi kama da cikin gida
  • Amma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun fara zargin yan Kwankwasiyya da kokarin bata masa suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dan majalisa wakilai mai wakiltar mazabar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini ya jawo magana bayan an hango wani bidiyonsa a kafafen sada zumunta.

A bidiyon da ya dauki hankali matuka, an hango Hon. Madakin Gini zaune da tulin kudi a gabansa da ake zaton sun kai miliyoyi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar Kwankwaso ta rikice, saɓani ya gifta tsakanin manyan NNPP

Madaki
Bidiyon Madakin Gini ya jawo surutai Hoto: @__yellows
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa, Aliyu Sani Madakin Gini da wasu da ba a san su waye ba su na kirga kudin yan dubu-dubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon dan majalisa ya jawo martani mm

Bidiyon da wani Gist lovers ta wallafa a shafin x, ya nuna Hon. Aliyu Sani Madakin Gini da wasu mukarrabansa su na gyara Naira.

Tuni masu amfani da shafin su ka fara tsokaci bisa yadda dan majalisar ya baje kudaden alhalin jama'a ba su da na abinci.

An zargi Kwankwasiyya kan bidiyon dan majalisa

Boss Mustapha a shafin X ya zargi yan Kwankwasiyya a Kano da kokarin bata sunan Aliyu Sani Madakin Gini saboda rikicinsa da Rabiu Kwankwaso.

Akalla mako biyu ke nan da Aliyu Sani Madakin Gini ya bayyana ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya, duk da ya jaddada cewa shi dan NNPP ne.

Yan majalisa sun fice daga Kwankwasiyya

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

A wani labarin kun ji cewa yan majalisar Kano guda biyu, Aliyu Sani Madakin Gini da Alhassan Rurum sun bayyana ficewa daga tafiyar Kwankwasiyya bisa zargin rashin adalci.

Aliyu Madakin Gini wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya fito fili ya nesanta kansa da Kwankwasiyya, ya zargi Sanata Kwankwaso da son kai.

Muhammad Malumfashi, babban Edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.