"An Samu Matsala": Jirgin Sama Ya Gamu da Matsala Yana daf da Tashi a Abuja

"An Samu Matsala": Jirgin Sama Ya Gamu da Matsala Yana daf da Tashi a Abuja

  • Jirgin sama na Air Peace ya gamu da tangarda a lokacin da yake shrin tashi daga birnin Abuja zuwa Legas da safiyar ranar Alhamis
  • Kamafanin sufurin jiragen saman Air Peace ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jirgin ya fasa tashi sakamakon farmakin wata tsuntsuwa
  • Ya kuma bai wa fasinjojin jirgin hakuri kan abin da ya faru, ya ce tuni aka kawo wani jirgin domin kwashe su zuwa wurin da suka nufa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani jirgin sama na kamfanin Air Peace ya gamu da tangarɗa yayin da yake shirye-shiryen tashi daga Abuja zuwa jihar Legas ranar Alhamis.

An ruwaito cewa jirgin ya gamu da tangarɗa ne yana dab da tashi sakamakon wata tsuntsuwa da ta gitta masa a filin sauka da tashi na Nnamdi Azikiwe.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda gwamnati ta tunkari matsalar tattalin arziki gaba gadi

Jirgin saman Air Peace.
Jirgin sama na Air Peace ya soke tashi sakamakon harin tsuntduwa a Abuja Hoto: Air Peace
Asali: Facebook

Yadda jirgin sama ya fasa tashi a Abuja

Lauya mai rajin kare hakkin dan adam ɗan asalin Legas kuma daya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin, Inibehe Effiong, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tsayar jirgin saman bisa tilas kuma ba zato ba tsammani ya jefa fasinjoji cikin firgici, inda wasu suka fara kururuwar neman agaji.

Kamfanin sufurin jiragen sama da Air Peace ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na Facebook, inda ya ba kwastomomi haƙuri.

Kamfanin jirgin sama ya bada haƙuri

A wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar da safiyar nan, ya ce tuni aka sauke fasinjojin da suka shiga jirgin kuma an mussanya masu wani jirgin.

Sanarwar ta ce:

"Muna sanar da fasinjojin mu cewa jirginmu da zai tashi daga Abuja zuwa Legas da ƙarfe 6:30 na safe ya gamu da tangarɗar farmakin tsuntsuwa kafin ya lula sama."

Kara karanta wannan

Gwamanti ta fara shirin karya farashin abinci, za a ba manoma tallafi

"Hakan ya sa jirgin ya juyo saboda lamarin tsaro kuma tuni aka sauke fasinjoji. Mun kawo wani jirgin domin tabbatar da cika muradan fasinjojinmu masu albarka."
"Muna fatan fasinjojin da lamarin ya shafa za su fahimci manufarmu da sauran waɗanda za su bi wasu jiragen waɗanda za a iya samun tsaiko saboda abin da ya faru."

Mutum 8 sun mutu a hatsarin jirgin sama

A wani rahoton, kun ji ana fargabar cewa fasinjoji shida da ma'aikatan jirgi sun mutu a hatsarin jirgin da ya faru a Ribas, a cewar rundunar 'yan sanda.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar tsaro ta tabbatar da mutuwar uku daga cikin fasinjojin, inda aka tsamo gawarwakinsu a kogi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262