Nuhu Ribadu Ya Fadi Makomar 'Yan Ta'addan Lakurawa a Najeriya
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya ja kunnen ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa da suka bayyana
- Nuhu Ribadu ya gargaɗi ƴan ta'addan da cewa sun zo a lokacin da ba za su kai labari ba domin shugaban kasa Bola Tinubu ne a kan mulki
- Hadimin shugaban kasar ya sha alwashin cewa za a fatattaki ƴan ta'addan da suka ɓulla a yankin Arewa maso Yamma daga Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi magana da kakkausar murya kan ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa.
Nuhu Ribadu ya gargaɗi ƴan sabuwar ƙungiyar da ke yankin Arewa maso Yamma cewa ƙarshensu ya kusa zuwa idan ba su daina ayyukan ta’addanci ba.
Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a wajen wani taro da shugaban hukumar kwastam ya shirya a Abuja a ranar Laraba, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Ribadu ya ce kan ƴan ta'addan Lakurawa?
Mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaro ya cika baki da cewa babu wanda ya taɓa ja shugaba Bola Tinubu kuma ya yi nasara.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ƙungiyar Lakurawa ba za ta kai labari ba domin ta zo a daidai lokacin da Tinubu ke kan karagar mulki.
Nuhu Ribadu ya kuma sha alwashin cewa za a kori ƴan ta'addan daga Najeriya.
"Waɗannan ƴan Lakurawan suna yin kuskure, babu wanda ya taɓa ja da Tinubu ya yi nasara."
"Sun zo a lokacin da ba za su kai labari ba, babu wanda ya taɓa yin nasara a kan Tinubu. Za mu fatattake su daga Najeriya."
- Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu ya kwatanta Tinubu da Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi wa tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari shagube kan tsaro idan aka kwatanta da kokarin gwamnati a yanzu.
Nuhu Ribadu, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya yi ikirarin cewa a yanzu Najeriya na da tsaro idan aka kwatanta da lokacin gwamnatin Buhari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng