'Yan Ta'adda Sun Kona Abincin N100m da Aka Bankawa Gonaki Wuta a Birnin Gwari

'Yan Ta'adda Sun Kona Abincin N100m da Aka Bankawa Gonaki Wuta a Birnin Gwari

  • Dan majalisar wakilai daga Birnin Gwari, Hon. Zubairu Birnin Gwari ya nemi daukin gwamnatin tarayya daga 'yan ta'adda
  • Hon. Zubairu Birnin Gwari ya ce mutanensa sun yi asarar akalla Naira miliyan 100 a harin da yan bindiga su ka kai Kaduna
  • Dan majalisar ya na ganin lokaci ya yi da jama'a za su fara kare kawunansu daga yan ta'adda idan gwamnati ta gaza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Dan majalisar Birnin Gwari da Giwa a majalisar wakilan kasar nan, Hon. Zubairu Birnin Gwari ya ce yan bindiga sun tafka mummunan barna a Kaduna.

Zubairu Birnin Gwari ya fadi haka ne bayan wasu miyagun yan ta’addan sun farwa gonakin jama’a a mazabarsa, su ka soye amfanin gona ta hanyar cinna wuta.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun ji ruwan alburusai, sun fara guduwa daga Najeriya

Kaduna
Manoman Kaduna sun yi asarar N100m Hoto: Legit.ng
Asali: Original

BBC ta wallafa cewa yan bindigar sun kone gonakin da ke Kwaga da Unguwar Zoko da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan ta’adda sun kona amfanin gonan N100m

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dan majalisar Kaduna a tarayyar Najeriya, Hon. Zubairu Birnin Gwari ya ce manoman da yan bindiga su ka farmaki gonakinsu sun tafka asara.

An samu rahotannin cewa harin da yan ta’adda su ka kai gonakin masara a yankin ya lakume akalla Naira miliyan 100.

Jama’a za su kare kansu daga yan ta’adda

Hon. Zubairu Birnin Gwari ya nemi daukin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wajen kawo karshen hare-haren yan bindiga a Kaduna.

Wakilin mazabar Birnin Gwari da Giwa a majalisar wakilai ya bayyana cewa matukar gwamnati ta yi biris da taimakon jama’a, za su fara kare kansu.

‘Yan ta’adda sun sha ruwan wuta

A baya mun wallafa cewa rundunonin sojojin kasar nan da na kasa sun yi wa sabuwar mayakan Lakurawa luguden wuta a jihar Kebbi, inda aka fatattake su zuwa iyakar Kwara da Benin.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun fara firgita jama'a, gwamnatin Tinubu ta fadi matakan da ta dauka

Kungiyar Lakurawa da aka fara jin karfinta a wasu jihohin Arewa maso Yamma na barazana ga tsaro lokacin da ake fama da 'yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.