Tinubu Ya Fadi Yadda Gwamnati Ta Tunkari Matsalar Tattalin Arziki Gaba Gadi

Tinubu Ya Fadi Yadda Gwamnati Ta Tunkari Matsalar Tattalin Arziki Gaba Gadi

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu tattalin arzikin Najeriya ya na kokarin durkushewa
  • Tinubu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a Edo yayin rantsar da sabon gwamnan jihar
  • Ya ce matakan da yan Najeriya su ke kuka da su sun zama dole, matukar ana so a ceto tattalin arziki daga karasa lalacewa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta karbi kasar nan a cikin durkushewar tattalin arziki.

Bola Ahmed Tinubu ya ce wannan ta sa gwamnatina ta dauki wasu tsauraran matakai da yan Najeriya ke kokawa da su a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya kafe a kan bakarsa, ya sake tunzura gwamnatin Tinubu

Tinubu
Tinubu a ce tattalin arziki ya na farfadowa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa shugaban kasar ya fadi haka ne a taron rantsar da gwamnan Edo, Monday Okpebholo da ya gudana ranar Talata a babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattalin arziki: Tinubu ya fadi kokarin gwamnatinsa

Arise Television ta wallafa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na sane da irin kalubalen da jama’a ke fuskanta saboda manufofinsa.

Amma ya nanata cewa sauki ya na nan tafe, domin tsare-tsaren da ya fitar za su tabbatar da tsamo tattalin arzikin kasa daga halin rugujewa da gwamnatinsa ta same shi.

Gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin saukin rayuwa

Shugaba Tinubu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashin Shettima ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu matakan da aka gani ne domin farfado da Naira.

Ya ce manufofin za su farfado da tattalin arziki ta hanyar samar da shimfida mai kyau da bayar da damammaki ga yan kasa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

Sarakuna sun tunkari Tinubu kan tsadar rayuwa

A wani labarin kun ji cewa sarakunan gargajiya a jihar Delta sun nemi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hanzarta fito da hanyar dakatar da wahala da yan kasa su ke sha.

Mai magana da yawun sarakunan, Luke Kalanama VIII ne ya shaidawa manema labarai cewa jama’a na cikin wani hali mara dadi, kuma dole sai gwamnati ta yi abin da ya dace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.