Zanga Zanga: Yaran Kano da Kaduna da Aka Sako Sun Ƙara Samun Tallafin Kudi

Zanga Zanga: Yaran Kano da Kaduna da Aka Sako Sun Ƙara Samun Tallafin Kudi

  • Tsohon gwamn jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya tallafawa kananan yaran Kano da Kaduna da aka sako, ya ba kowane N50,000
  • Jami'an tsaro sun cafke yaran su 119 a lokacin zanga-zanga bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu
  • Gidauniyar Bafarawa ta roki yaran su yi amfani da tallafin wajen kama sana'o'i domin dogaro da kansu, su kaucewa zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Yaran Kano da Kaduna da aka sako bayan tsare su na tsawon lokaci na ci gaba da samun tausayawa da shugabanni da manyan ƴan siyasa a Arewacin Najeriya.

Idan za ku iya tunawa ƙananan yaran sun shiga hannun jami'an tsaro ne a lokacin zanga-zangar da aka yi a watan Agustan da ya shuɗe.

Attahiru Bafarawa.
Tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya tallafawa kananan yaran Kano da Kaduna da aka sako Hoto: Attahiru Bafarawa/Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Yaran Kano da Kaduna sun samu tallafi

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta yi karin bayani, ta fadi wanda ta kama lokacin zanga zanga

Gidauniyar tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa ta ba kowane ɗaya daga cikin yaran da aka sako tallafin N50,000, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin jagororin gidauniyar, Dr Sulieman Shuaibu, shi ne ya miƙa tallafin a madadin tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa.

Da yake jawabi, Dr. Sulieman ya ce sun ba yaran wannan tallafi ne domin karfafa masu guiwa su dogara da kansu ta hanyar fara ƙananan sana'o'i.

Ya ce:

"Ba mu goyon bayan abin da kuka yi amma manufarku mai kyau ce, mai girma tsohon gwamnan ba ya tare da yin zanga-zanga amma ya amince da bin wasu hanyoyin don isar za koke.
"Ya ba mu umarni a madadin gidauniyarsa da mu ba kowannenku tsabar kudi N50,000, sannan yana rokon maimakon zanga-zanga ku dage da yi wa ƙasa addu'ar samun zaman lafiya.

Zanga-zanga: Yaran sun yi wa Bafarawa godiya

Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar masu zanga-zangar #EndBadGovernance, Abubakar Ishaq, ya godewa gidauniyar da ta kawo musu dauki. 

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

Ya ce wannan tallafi zai taimaka masu matuka a kokarinsu na farfaɗowa daga halin da suka tsinci kansu, kana su dogara da kansu.

Abubakar ya buƙaci ƴan uwansa ƴan kungiyar da su yi taka-tsan-tsan a nan gaba wajen yanke shawarar matakin da za su ɗauka.

Yaran da aka tsare sun yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa yara da dama da aka cafke saboda zanga-zanga sun bayyana irin wahalar da suka sha lokacin da aka tsare su.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi musu afuwa bayan sun kwashe kwanaki masu yawa a tsare a hannun jami'an tsaron Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262