Masu Zanga Zanga Sun Taso Tinubu a Gaba, Ana So Ya Kori Dan Arewa daga Minista

Masu Zanga Zanga Sun Taso Tinubu a Gaba, Ana So Ya Kori Dan Arewa daga Minista

  • A ranar Talata ne daruruwan mutane daga Zamfara suka gudanar da zanga-zanga a Abuja domin neman tsige Bello Matawalle
  • Masu zanga zangar sun zargi Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar da haifar da ƙarin matsalar tsaro a garuruwan Zamfara
  • Sun bukaci shugaba Bola Tinubu da ya kori Matawalle daga mukamin ministan tsaro tare da ba DSS damar gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Daruruwam mata da maza daga jihar Zamfara sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta korar Bello Matawalle daga kujerar minista.

A yayin wata zanga-zanga a hedikwatar DSS a Abuja, wasu mazauna Zamfara sun nuna rashin jin daɗi game da matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Masu zanga zanga sun yi magana kan matsalar tsaron Zamfara, sun aika sako ga Tinubu
Masu zanga zanga sun bukaci Tinubu ya kori Matawalle daga ministan tsaro. Hoto: @Bellomatawalle1, @officialABAT
Asali: Facebook

Mazauna Zamfara sun yi zanga zanga

Jaridar Punch ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun yi zargin cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ne ke haifar da ƙarin ayyukan ‘yan ta'adda a Zamfara.

Kara karanta wannan

Matawalle: Zanga zangar neman bincikar minista ta barke a DSS, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa alaƙar Matawalle da ‘yan bindigar a lokacin mulkinsa tana daga cikin dalilan da suka haifar da ƙarin matsalar tsaro a jihar.

Masu zanga-zangar, da suka dura ofishin DSS a cikin bas 12 , sun daga tutoci da rubutun "ana ta kashe mu" da "DSS, ku ceci mu daga ‘yan bindiga," inji rahoton The Cable.

An bukaci Tinubu ya kori ministan tsaro

Shugaban masu zanga-zangar, Mallam Musa Mahmud, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya ki korar Matawalle daga ministanssa.

Mallam Musa ya ce hujjojin da Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya gabatar sun isa su sanya shugaban kasar ya tsige Matawalle daga mukaminsa.

“Ya kamata hukumar DSS ta baiwa Shugaba Tinubu shawarar ya sauke Matawalle daga mukaminsa, domin ya fuskanci kwamitin bincike."

- A cewar Malam Musa.

Mahmud ya nemi a gudanar da bincike kan Matawalle, yana mai cewa bai kamata biyayyarsa ga Tinubu ta ba shi kariya daga tuhuma kan zargin da ake yi masa ba.

Kara karanta wannan

Asalin Lakurawa da shirin da sojojin Najeriya suka yi na kawo karshen ƴan ta'addan

Dalilin Tinubu na ƙin korar Ministan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya samu labaran zargin da ake yi wa Bello Matawalle na ɗaukar nauyin ƴan bindiga a Zamfara.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnati ta gudanar da bincike kan wadannan zarge-zarge kuma ta gano babu gaskiya a ciki, shi ya sa ba a tsige Matawalle daga minista ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.