'Bunkasa Aikin Ƴan Sanda,' Gwamnan Kano Ya Dauki Matakan Dakile Matsalar Tsaro

'Bunkasa Aikin Ƴan Sanda,' Gwamnan Kano Ya Dauki Matakan Dakile Matsalar Tsaro

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ba da kyautar sababbin motocin sintiri guda 78 ga rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano
  • Gwamnan ya ce motocin za su inganta tsaro a dukkanin kananan hukumomin jihar, inda kowane DPO zai samu mota daya
  • Gwamna Yusuf ya godewa jami’an tsaro bisa sadaukarwarsu, yana mai jaddada cewa tallafin ba shi da wata alaka da siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon motoci 78 ga rundunar 'yan sanda ta Kano, domin inganta tsaro a fadin jihar.

Bikin ba da kyautar motocin wanda ya gudana a gidan gwamnati, ya nuna mataki mai mahimmanci na karfafa tallafi ga jami'an tsaron Kano.

Gwamnan Kano ya dauki matakan dakile matsalar tsaro a fadin jihar
Gwamna Abba ya ba 'yan sandan Kano kyautar motoci. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Kano: Abba ya ba 'yan sanda motoci

A cewar sanarwar da gwamnan ya fitar a shafinsa na X, motocin sun hada da Toyota Hilux guda 44 da Sharon guda 34, kuma za a raba su a kananan hukumomi 44 na Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ya runtumo bashin biliyoyin Naira daga ƙasar Faransa? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Gwamna Abba ta ce kowane 'DPO' zai samu mota daya don saukaka ayyukansu na yau da kullum da inganta daukar matakin gaggawa kan batutuwan tsaro.

Gwamna Abba Yusuf ya jaddada cewa wannan gudunmawa wani bangare ne na kudirin inganta kayan aikin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a Kano.

Gwamnan Kano ya gargadi masu aikata laifi

Abba ya kuma bayyana cewa wannan shirin tallafin ba shi da wata alaka da siyasa, kuma an yi shi ne kawai don tabbatar da tsaron mutanen jihar Kano.

A lokacin taron mika motocin, gwamna Abba Yusuf ya gargadi masu aikata laifi da su nisanci Kano, yana jaddada kudurin gwamnati na kare rayuka da dukiyar jama'a.

Gwamnan ya kuma gode wa rundunar 'yan sanda da sauran hukumomi bisa jajircewarsu wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kano.

Gwamna Abba ya yi ta'aziyyar 'yan sandan Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati, sun ziyarci rundunar ƴan sanda domin ta'aziyyar jami'an da suka rasu.

Kara karanta wannan

Ana kukan Lakurawa sun fara karfi a Sokoto, gwamna ya gana da ministan Tinubu

Gwamnan na Kano, ya jajantawa iyalan ƴan sanda biyar da suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Karfi da ke kan hanyar Kano zuwa Zaria.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.