"Babu Mai Yin Barci": Minista Ya Fadi Kokarin Gwamnatin Tinubu kan Magance Rashin Tsaro
- Ministan harkokin cikin gida na Najeriya ya yi magana kan ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin magance matsalar rashin tsaro
- Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan ba sa yin barci domin ganin an magance matsalar da ake fama da ita
- Ministan ya ba da tabbacin cewa an samu ci gaba sosai wajen rage matsalar rashin tsaro tun bayan zuwan gwamnatin shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin magance matsalar rashin tsaro.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na yin namijin ƙoƙari wajen ganin ta shawo kan ƙalubalen rashin tsaron da ya addabi ƙasar nan.
Olabunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu na ƙoƙari kan rashin tsaro
Ministan ya bayyana cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ministan tsaro, Mohammed Badaru da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, ba sa yin barci saboda matsalar.
"Babu wanda yake hutawa. Babu NSA Mallam Nuhu Ribadu, babu ministan tsaro ba, ba babban hafsan hafsoshin tsaro ba, ba hukumar DSS ba."
"Babu wanda yake barci, muna aiki. Wannan batu na tsaro babban al’amari ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya, kuma ba zan zauna a nan na ƙi ɗaukar alhakin tsaron ƴan Najeriya a madadin shugaban ƙasa ba."
- Olubunmi Tunji-Ojo
Tsaro ya inganta a mulkin Tinubu - Minista
Ya bayyana cewa an samu ingantuwar tsaro a ƙasar nan tun bayan hawan gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya nuna cewa dakarun sojojin Najeriya sun rage ƙarfin ƴan ta'addan ISWAP da na Boko Haram.
An ba Shugaban kasa Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar cigaban Arewa ta Tsakiya (MBF) ta yi kira na musamman ga Bola Ahmed Tinubu kan tsare tsaren tattali da ya kawo.
Ƙungiyar MBF ta ce a halin da ake ciki tattalin arziƙin yan Najeriya ya ruguje kuma suna bukatar samun tallafi daga gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng