Sojoji Sun Kama Gungun Yaran Ƙasurgumin Ɗan Bindiga John Gata

Sojoji Sun Kama Gungun Yaran Ƙasurgumin Ɗan Bindiga John Gata

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a kan wasu tarin yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Taraba
  • Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun yi musayar wuta ne kafin su kama da dama cikin gungun yan bindigar da kayayyakinsu
  • Binciken jami'an tsaro ya tabbatar da masu garkuwa da mutane 12 da aka kama suna cikin gungun dan bindiga da ake nema ido rufe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Sojojin Najeriya a jihar Taraba sun samu nasara kan wasu yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun samu kiran gaggawa ne a ƙauyen Chachanji yayin da miyagun suka je yin garkuwa da mutane.

Sojoji
Sojoji sun kama yan bindiga a jihar Taraba. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Jaridar Punch ta wallafa cewa dakarun sojin Najeriya sun kwato babura da wasu kayyakki daga wajen yan ta'addar.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun haɗa kai, sun tunkari Bola Tinubu kan tsadar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kama yaran John Gata

The Sun ta wallafa cewa a ranar 7 ga watan Nuwamba sojojin Najeriya suka samu kira cewa masu garkuwa da mutane sun sace mutane biyu a Chachanji na jihar Taraba.

Sojoji sun fafata da yan bindigar wanda daga nan miyagun suka tsere cikin daji suka bar wasu daga cikin makamansu.

Bayan haka, sojoji sun tunkari wajen da yan bindigar ke shaye shaye wanda a wajen aka kama mutum 12 a cikin wadanda ake zargi da garkuwa da mutanen.

"Bayan bincike mai zurfi, mutanen da aka kama sun ce suna cikin gungun masu garkuwa da mutane.
Haka zalika an gano cewa suna cikin yaran ƙasurgumin ɗan bindiga da yake ta'addanci a Taraba da Benue, Veior John Gata."

- Rundunar sojin Najeriya

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwato babura 14 wajen waɗanda ake zargi da garkuwa da mutanen.

An kashe masu karɓar haraji a Delta

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan bindiga sun bude wuta kan masu karbar haraji a jihar Delta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a babbar kasuwar karamar hukumar Ughelli kuma an kashe masu karɓar haraji biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng