Ana Surutun Musuluntar da Najeriya, Tinubu Ya Zauna da Yarima Mohammed a Saudiyya

Ana Surutun Musuluntar da Najeriya, Tinubu Ya Zauna da Yarima Mohammed a Saudiyya

  • Shugaban kasar nan, Bola Ahmed Tinubu ya zauna da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud
  • Zaman na zuwa duk da cewa wasu daga yan Najeriya na ganin rashin dacewar yadda Tinubu ya halarci taron Musulmi da Larabawa
  • Shugabannin sun tattauna yadda za a kyautata alaka ta fuskoki da dama tsakanin kasashen biyu da zummar kawo cigaba Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Riyadh Sadia – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman AbdulAzizi Al Saud a kasar Saudiyya.

Zaman shugabannin biyu na zuwa a lokacin da wasu daga cikin yan kasar nan ke ce-ce-ku-ce kan halartar taron kasashen Larabawa da na Musulmi a kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

An soki Tinubu kan wakiltar Najeriya a taron kasashen Musulmi da Larabawa

Tinubu
Yariman Saudiyya ya gana da Tinubu Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Jaridar Saudiyya ta ruwaito cewa Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud da Bola Tinubu sun tattauna a gefen taron kasashen Larabawa da Musulmi da aka kammala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya gana da Yariman Saudiyya

Jaridar The Nation ta wallafa cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya nemi hadin kan kasar Saudiyya bayan ya tattauna da Yarima mai jiran gado na kasar.

Wannan na zuwa bayan shugaba Tinubu goyi bayan Saudiyya na cewa ya dace kasar Isra’ila ta dakatar da yakin da ta ke kai wa kan Falasdinawa, musamannan na zirin wanda ke zirin Gaza.

Abin da Tinubu ya tattauna da Yarima

Kasar Saudiyya da Najeriya sun tattauna hanyoyin da kasashen biyu za su kara hadin kai da bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu.

Wasu daga cikin wanda su ka halarci taron sun hada da Ministan a Saudiyya, Yarima Abdullah bin Bandar bin Abdulaziz da Ministan tsaro, Khalid bin Salman bin Abdulaziz,.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

An soki Tinubu kan zuwa Saudiyya

A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasar nan, Cif Charles Udeogaranya ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da rashin mutunta kundin mulkin Najeriya.

Cif Charles Udeogaranya ya bayyana takaici, inda ya ce Najeriya ba musulmar kasa ba ce, kuma addini ba ya tasiri, saboda haka bai dace a ga kasar nan a kasar Saudiyya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.