Gwamnatin Abba Ta Fadi Basussukan da Ta Biya Wadanda Ta Gada Wajen Ganduje

Gwamnatin Abba Ta Fadi Basussukan da Ta Biya Wadanda Ta Gada Wajen Ganduje

  • Ofishin kula da basussuka na jihar Kano ya bayyana adadin lamunin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya waɗanda ta gada
  • Shugaban ofishin ya bayyana cewa gwamnatin ta biya basussukan da suka kai N63bn na cikin gida da na ƙasashen waje
  • Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Abba ba ta karɓo ko sisi da sunan bashi ba tun bayan hawanta kan mulki a shekarar 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ofishin kula da basussuka na jihar Kano ya bayyana basussukan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya waɗanda ta gada daga wajen Abdullahi Umar Ganduje.

Ofishin ya bayyana cewa ya biya N63,508,024,580.03 na basussukan cikin gida da na ƙasashen waje waɗanda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta karɓo.

Gwamnatin ta biya basussukan Ganduje
Gwamnatin Abba Kabir ta biya wasu daga cikin basussukan da Ganduje ya karbo Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, OFR
Asali: Twitter

Darakta Janar na ofishin kula da basussuka na jihar Kano, Dakta Hamisu Sadi Ali ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan tashin bam a babban birnin jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba ta biya basussukan Kano

Ya ce a yayin da gwamnatin Abba ta gaji basussuka masu ɗimbin yawa, ta rage yawansu sosai, inda ya ce gwamnati mai ci ba ta karɓo wani bashi ba.

Dakta Hamisu Sadi Ali ya bayyana cewa tun zuwan gwamnatin Abba a watan Mayun 2023 har ya zuwa yanzu ba ta taɓa karɓo ko sisi a ciki ko wajen Najeriya da sunan bashi ba.

"A ƙoƙarinsa na rage basussukan da jiharmu ke fama da su, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya bashin waje na N3,491,137,226.73 da bashin cikin gida na N60,016,887,353.57 wanda ya kai jimillar N63,508,024,580.03 a wata shidan farko na shekarar 2024."
"Da wannan ci gaban, basusukan da ke bin mu na cikin gida da na ƙasashen waje sun ragu sosai zuwa N127,793,608,048.62."

- Dakta Hamisu Sadi Ali

Ganduje ya caccaki masu son a hukunta shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya magantu kan kiran cafke tsohon gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Abba ya ɗauki zafi, ya yi magana kan daina ɗaga kiran Kwankwaso

Oliver Okpala ya caccaki masu kiran a kama Ganduje inda ya ce ba mai cin mutuncinsa a yanzu domin lamarin zargin da ake yi masa na gaban kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng