Kamfanin NNPCL Ya Yi Magana kan Shigo da Man Fetur daga Ƙasashen Ƙetare
- Shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana cewa sun daina shigo da tataccen man fetur daga ketare
- Kyari ya kuma musanta cewa NNPCL na nuna adawa ga matatun man cikin gida kamar matatar Alhaji Aliko Ɗangote
- Ya ce kamfanin ya san abin da ya kamata don haka babu bukatar sai ƴan Najeriya sun masu ca kan abin da tun asali sun san amafaninsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya daina shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen ƙetare zuwa Najeriya.
Shugaban NNPCL, Mele Kyari ne ya bayyana hakan da yake jawabi a wurin taron kungiyar NAPE karo na 42 wanda aka yi a jihar Legas ranar Litinin.
Ya bayyana cewa yanzu kamfanin NNPCL na sayen man fetur daga matatun mai na cikin gida, ciki har da matatar man Dangote, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A halin yanzun kamfanin NNPCL ya daina shigo da mai, mun dawo saye a matatunmu na cikin gida," in ji Kyari.
Kamfanin NNPCL na yi wa Ɗangote zagon ƙasa?
Haka nan kuma shugaban kamfanin man ya musanta zargin cewa NNPCL na yi wa matatun cikin gida kamar matatar Ɗangote bakin ciki da zagon ƙasa.
Mele Kyari ya ce raɗe-raɗin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne domin suna alfahari da gina matatar mai mai girma da hamshakin attajiri, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi.
NNPCL na ba matatar Ɗangote ɗanyen mai?
Shugaban NNPCL ya jaddada cewa ba su bukatar sai wani ya gaya masu ga yadda za su yi kasuwanci da matatun cikin gida, ba wai ta Ɗangote kaɗai ba.
A rahoton The Nation, Kyari ya ce:
"Tun farko, mun san cewa yana da amfani mu sayarwa matatun cikin gida danyen mai, don haka ba ma bukatar a shawo kan mu, ba mu bukatar wani ya mana magana."
Matasa sun nemi a sauke shugaban NNPCL
A wani rahoton, an ji cewa gungun masu zanga-zanga sun durfafi Majalisar Tarayya domin bukatar a kori shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.
Matasan da ke wakiltar kungiyoyi sun bukaci Bola Tinubu ya gargadi Kyari kan tsare-tsare da za su jefa al'umma cikin kunci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng