Asalin Lakurawa da Shirin da Sojojin Najeriya Suka Yi na Kawo Karshen Ƴan Ta'addan

Asalin Lakurawa da Shirin da Sojojin Najeriya Suka Yi na Kawo Karshen Ƴan Ta'addan

  • Rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da babban aikin kawar da Lukurawa, sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ta bayyana
  • Wannan ƙungiyar ta sami damar shigowa Najeriya ne ta hanyar haɗin gwiwa da mayaƙan jihadi daga Mali, Libya da kuma Nijar
  • An ce Lakurawa ta haɗa kai da ’yan bindigar gida, inda take jan hankalin matasa tare da shirin fadada ayyukanta na ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sojojin Najeriya sun kaddamar da babban hari domin dakile Lakurawa, wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ke barazana ga tsaron ƙasar nan.

An ce kungiyar Lakurawa ta kunshi mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyoyin jihadi daga Mali, Libya, da Nijar da suka samu matsuguni a Arewacin Najeriya.

Sojojin Najeriya sun yi babban shiri na kawo karshen kungiyar ta'addanci ta Lakurawa
Sojoji sun dauki matakin kawar da 'yan ta'addan Lakurawa daga Arewacin Najeriya. Hoto: Audu Marte/AFP
Asali: Getty Images

Asalin Lakurawa da korarsu daga Sokoto

Da farko, wasu garuruwan Fulani ne suka yi hayar mayaka daga ƙasashen waje domin su kare su daga ’yan fashi da ke satar shanunsu, a cewar sanarwar rahoton @DefenseNigeria.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun zo da ta'addanci, sun yi barna a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadannan mayaƙa sun sami amincewar mutane kuma sun fara samun matsuguni a cikin al’umma, inda suke kara samun goyon baya ta hanyar kwarewar aikinsu.

Sai dai, a 2018, gwamnan Sakkwato ya kore su daga jiharsa, lamarin da ya dakile tasirinsu na ɗan wani lokaci tare da hana su kafa sansani na dindindin.

Yadda Lakurawa suka dawo jihar Sokoto

Juyin mulki na watan Yuli 2023 da ya faru a Nijar ya canza al’amura, ya kawo ƙarshen haɗin kan yaki da tsaron iyakokin kasa, wanda ya ba 'yan ta'adda damar watayawa.

Iyakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar, mai nisan fiye da kilomita 1,600 ta zama cibiyar aikata laifuffuka na ƙasa da ƙasa, ciki har da ta’addanci.

Mayakan da aka kora daga Sokoto sun yi amfani da barakar tsaron da aka samu wajen dawowa Sokoto tare da kafa Lakurawa, suna ƙoƙarin faɗaɗa tasirinsu.

An ce mayakan Lakurawa, sun yi amfani da dabaru daban-daban, ciki har da hada kai da ’yan fashi na gida, suna jan ra'ayin matasa da kudi da kuma kalmomin jihari.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan saukar dusar ƙanƙara a ɗakin Ka'aba

Sojoji sun dauki mataki kan Lakurawa

Sai dai kuma, an rahoto cewa sojojin Najeriya sun kaddamar da wani atisaye na musamman, da nufin kakkabe wadannan 'yan ta'adda daga Arewa maso Yamma.

An ce sojojin sun raunana dukkanin wasu hanyoyin ’yan fashi ta hanyar hare-hare da suka kai, har sun kashe fitattun shugabanni, wannan ya sa Bello Turi tserewa.

Yanzu kuma sojojin na fuskantar Lakurawa, wata babbar barazana ga tsaron Arewa da kasar baki daya, amma dai, sojojin na fatan ganin karshen kungiyar cikin gaggawa.

Lakura na shirin aika sako ga Turji

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kungiyar Lakurawa, Habib Tajje zai tura sakon gargadi ga kasurgumin dan bindiga, Bello Turji.

An ce, kungiyar Lakurawa, za ta dauki matakin aika sako ga Bello Turji ne domin bukatar ya janye dukan ayyukan ta'addanci da yake yi a Arewacin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.