'Yan Boko Haram Sun Zo da Ta'addanci, Sun Yi Barna a Borno
- Mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun kai hari a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
- Ƴan ta'addan sun hallaka mutum uku a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar a daren Lahadi
- Tsagerun masu tayar da ƙayar bayan sun kuma yi awon gaba da masunta masu yawa bayan sun kai harin a cikin dare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Mayaƙan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutane uku a wani hari da suka kai a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kuma yi garkuwa da masunta sama da 12 a harin wanda suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno a daren ranar Lahadi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kai harin ne a wani ƙauye mai suna Malam Yawri, mazaɓar Cross Kawu, kusa da tafkin Chadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan Boko Haram suka kai harin
A cewar majiyar civilian JTF, ƴan ta'addan na Boko Haram sun iso ne da misalin ƙarfe 11:45 na dare, suka tattaro mutanen ƙauyen, sannan suka kashe masunta guda biyu.
Rahotanni sun ce sun yi awon gaba da wasu mutum 13, sannan daga baya an gano ƙarin gawa a cikin daji.
Wani jami’in ƙaramar hukumar ya tabbatar da cewa an ga wasu ƴan ta’adda da dama a kewayen Jemu na Cross Kawu.
Jami’in ya bayyana damuwarsa kan tsaron mazauna yankin, ya kuma yi kira ga sojoji su gaggauta kawo musu ɗauki.
Lamarin dai ya biyo bayan farmakin da dakarun kasar Chadi suke kai wa ƴan Boko Haram, wanda ya sa suka fatattaki ƴan ta’addan zuwa ƙaramar hukumar Kukawa, inda ake kyautata zaton cewa da dama sun samu mafaka.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'addan ISWAP.
Dakarun sojojin sun kai hare-haren ne a kudancin tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta'adda masu yawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng