Kwastam Ta Kama Fetur na Miliyoyin Naira, Za a Kara Jefa Yan Kasa cikin Wahala
- Hukumar kwastam ta kasa ta bayyana gagarumin aikin da ta ke na dakile safarar man fetur zuwa kasashen ketare
- An kama masu kokarin fasa kwaurin fetur da ya kai lita 67,000 a iyakar Neja da Kwara ana kokarin fitar da shi waje
- An yi kamen ne a lokacin da yan kasar nan ke kokawa da karancin fetur da wahalarsa duba da yadda aka kara farashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kwara – Yayin da yan kasa ke kuka da karancin fetur, jami’an hukumar kwastam sun damke masu safararsa zuwa kasar waje.
Jami’an hukumar da ke aiki karkashin shirin Operation Whirlwind sun bayyana yadda su ka yi ram da dubban litar fetur.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an kimanta fetur da jami’an kwastam su ka kama ya kai N84,870,000 a kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwastam ta kama masu safarar man fetur
Hukumar kwastam ta kasa ta ce jami’anta sun kama masu safarar fetur da litar mai 67,000 a hanyar fitar da shi daga Najeriya.
Hukumar ta fadi yadda ta ke gudanar da aikin dakile safarar kaya da hukumomin kasar nan su ka haramta, daga ciki har da fetur.
Hukumar Kwastam ta yi kame a iyakar Kwara
Jami'an kwastam ta ce jami’anta sun yi nasarar kare kasar nan daga tafka asara ta hanyar safarar kayayyaki zuwa kasashen waje.
Hukumar ta ce ta hana fitar da fetur ta iyakar Neja zuwa Kwara, tare da damke masu kokarin fitar da fetur da wasu kayayyakin zuwa wajen kasar nan.
Hukumar kwastam ta cafke man fetur
A wani labarin kun ji cewa hukumar kwastam ta damke man fetur na da wasu bata-gari ke kokarin fitarwa ta iyakar jihar Adamawa zuwa kasar Kamaru yayin da yan kasa ke koka.
Shugaban hukumar kwastam da ke kula da jihohin Adamawa da Tarana, Garba Bature ne ya bayyana haka, inda ya nanata cewa ba za su kara bari ana cutar da yan kasar nan ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng