'Babu Yadda Aka Iya da Ni': Ganduje Ya Yi Martani kan Korafin da Aka Kai a EFCC
- Yayin da aka kai korafi gaban EFCC kan tuhumar shugaban APC, Abdullahi Ganduje, hadiminsa ya yi magana
- Oliver Okpala ya caccaki wadanda suka shigar da korafin, ya ce ba su mutunta doka ba saboda lamarin na gaban kotu
- Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin yaki da cin hanci 51 sun yi korafi ga EFCC kan tuhume-tuhume da ake yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hadimin shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya magantu kan kiran cafke tsohon gwamnan Kano.
Oliver Okpala ya caccaki masu kiran a kama Abdullahi Ganduje inda ya ce babu mai cin mutuncinsa a yanzu.
An bukaci EFCC ta yi ram da Ganduje
Hadimin tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Litinin 11 ga watan Nuwambar 2024, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kiran cafke Ganduje da wasu kungiyoyin yaki da cin hanci suka yi kan badakalar Ganduje.
Kungiyoyin akalla 51 sun bukaci hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta yi gaggawar kamawa da hukunta Ganduje.
Har ila yau, sun bukaci hukumar ta tabbatar da yin gaskiya da adalci yayin binciken domin hukunta shi daidai da laifinsa, Vanguard ta ruwaito.
Ganduje ya yi martani kan zargin cin hanci
Sai dai Okpala ya ce babu mai cin zarafin Ganduje, ya ce masu korafi sun manta da lamarin na gaban kotu a yanzu.
"Mun samu labarin wasu kungiyoyin yaki da cin hanci 51 na korafi ga EFCC domin kama shugaban APC, Abdullahi Ganduje."
"Idan aka yi duba zuwa ga korafinsu, za ka gane cewa sun yi nisa wurin bata sunan wasu ne kawai."
"Ya tabbata ba su mutunta dokokin kasa kuma ba su yi duba zuwa ga abubuwan da ke gaban kotu ba."
"Ya kamata irin wadannan matsaloli ba a tattauna su a yanzu duba da cewa lamarin na gaban kotu da gwamnatin jihar Kano ta shigar."
- Oliver Okpala
APC ta yi magana kan tsige Ganduje
Kun ji cewa APC ta fara samun saukin rikicin shugabanci bayan kungiyar jam'iyyar, reshen Arewa ta Tsakiya ta zubar da kayan yakinta.
Kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya na fafutukar cire Abdullahi Umar Ganduje daga mukaminsa saboda zargin rashin dacewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng