Ana Tsoron Wani Abin Fashewa Ya Tarwatse a Babban Birnin Jiha a Arewa
- Ana fargabar tashin bom a Jos, babɓan birnin jiha% Filato ranar Talata a kusa da wata kasuwa da ta saɓa tara jama'a da yawa
- Rundunar ƴan sanda reshen jihar Filato ta musanta raɗe-raɗin tashin bom a Jos, ta ce mutane ne sjka tsorata da abin da ba zai masu lahani ba
- Gwamnatin Filato ta tabbatar da al'umma cewa za ta ba su kariya, sannan ta yabawa hukumomin tsaro bisa ɗaukar matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, jihar Plateau - Mutane sun shiga firgici da ruɗani yayin da aka fara yaɗa raɗe-raɗin tashin bom a Jos, babban birnin jihar Filato.
Wansu ganau sun ce ƴan sandan sashin kwance bom sun kai ɗauki wurin da aka ga wani abu da ake zargin abin fashewa ne a kusa da wata kasuwa.
A rahoton Channels tv, tawagar kwance bom daga rundunar ƴan sanda sun yi nasarar warware abin da ake zaton bom ne kuma sun ɗauke sauran ababen da ake tsoro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun musanta fashewar bom
Sai dai rundunar ƴan sanda reshen jihar Filato ta yi gaggawar kwantar da hankulan jama'a, inda ta bayyana zargin tashin bom da ƙarya mara tushe, rahoton Daily Trust.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan, Alfred Alabo, ya ce:
"Nan take bayan samun labarin, kwamishinan ƴan sanda na Filato, Emmanuel Adesina ya tura tawagar kwance bom zuwa wurin."
"Bayan gudanar da bincike a tsanake, jami'an tsaron sun gano cewa babu bom a wurin kwata-kwata.
Gwamna Muftwang ya yi maagana
Da yake martani a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Gwamna Caleb Mutfwang ya kwantar da hankulan jama'a da cewa babu wani abin fargaba.
Gwamnan ya ce:
"Rashin fahimta ne, wasu nutane ne suka fara fassara wata jaƙar ledoji fassarar bom ne, wanda hakan ya haifar da tsoro a zuƙatan jama'a."
Ƴan sanda sun gwabza da miyagu a Jos
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jijar Plateau sun yi artabu da wasu masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Ƴan sandan bayan fafatawa da masu garkuwa da mutanen sun samu nasarar kuɓutar da wani matashi da suka sace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng