IPMAN: 'Yan Kasuwa Sun ce Farashin Fetur zai Karye bayan Daidaitawa da Dangote
- Kungiyar yan kasuwa masu harkar man fetur (IPMAN) ta yi albishirin samun sauƙin kudin fetur bayan tattaunawa da matatar Dangote
- IPMAN ta ce a yanzu haka ta warware duk wani sabani da ke tsakaninta da matatar Dangote kuma za ta fara ɗaukar fetur daga matatar
- Kungiyar ta IPMAN ta kara da cewa yarjejeniyar da suka yi da matatar Dangote zai sanya samun man fetur a wadace a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FTC, Abuja - Kungiyar yan kasuwar man fetur (IPMAN) ta yi magana kan farashin fetur bayan yin yarjejeniya da matatar Dangote.
IPMAN ta ce yan Najeriya za su amfana sosai a dalilin yarjejeniyar da suka samu nasarar kullawa da matatar Dangote.
Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Garima ne ya bayyana haka a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IPMAN ta ce farashin man fetur zai sauka
Kungiyar IPMAN ta yi albishir da cewa za a samu saukin farashin man fetur a gidajen man Najeriya.
Shugaban kungiyar, Abubakar Garima ne ya bayyana haka, ya ce yarjejeniyar da suka yi da matatar Dangote ne za ta jawo saukin.
Leadership ta wallafa cewa Alhaji Abubakar Garima ya ce a yanzu haka sun yi yarjejeniyar da za ta ba su damar sayen man fetur da sauran kayyakki daga matatar Dangote.
"Yarjejeniyar da muka yi da matatar Dangote za ta taimaka wajen wadatar da yan Najeriya da man fetur.
Bayan wadatar man fetur, yan Najeriya za su samu mai a farashi mai rahusa."
- Abubakar Garima, shugaban IPMAN
Amfanin yarjejeniyar Dangote da IPMAN
Kungiyar IPMAN ta ce za ta cigaba da goyon bayan matatar Dangote domin yadda ta ke samar da ayyukan yi a Najeriya.
Wani masanin tattali, Kelvin Emmanuel ya ce yarjejeniyar za ta rage matsaloli a harkar musamman lura da cire NNPCL daga shiga tsakanin IPMAN da matatar Dangote.
Tsadar mai ya jawo tafiya da kafa a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa hauhawar farashin man fetur ya tilastawa mazauna Kano amfani da kekuna, baburan lantarki ko tafiya a kasa.
Rahoto ya nuna cewa an samu karancin motoci a kan titunan jihar Kano yayin da jama'a ke neman sauki kan tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng