Ana Kukan Lakurawa Sun Fara Karfi a Sokoto, Gwamna Ya Gana da Ministan Tinubu
- Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya gana da ministan kudi, Mista Wale Edun, domin tattauna hanyoyin ci gaban arzikin jihar
- Gwamna Ahmad ya ce sun tattauna kan dabarun da za su inganta tattalin arziki, kyautata ababen more rayuwar 'yan jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni suka bayyana cewa sabuwar kungiyar Lakurawa ta fara karfi a garuruwan jihar Sokoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya gana da ministan kudi, Mista Wale Edun, domin tattauna muhimman hanyoyin hadin kai da taimakekeniya.
A yayin ganawar, gwamnan da ministan sun tattauna kan dabarun da za su inganta ci gaban tattalin arziki, kyautata ababen more rayuwa a jihar Sokoto.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai girma gwamnan ya fitar a shafinsa na X a daren ranar Litinin, 11 ga Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Sokoto ya gana da ministan kudi
Sanarwar gwamnan ta ce:
"A safiyar yau, na samu damar ganawa da ministan kudi, Mista Wale Edun, domin tattauna muhimman hanyoyin hadin kai da goyon baya.
"A lokacin ganawar, mun tattauna kan dabarun da za su inganta ci gaban tattalin arziki, kyautata ababen more rayuwa da bunkasa ayyukan da suka dace ga al'umma."
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta fahimci muhimmancin daidaita tsarin kudi domin tabbatar da cewa jihar Sokoto na samun tallafi daga gwamnatin tarayya.
Gwamna ya fadi manufar alakarsa da tarayya
Sanarwar gwamnan ta ce hadin guiwa tsakanin Sokoto da gwamnatin tarayya zai samar da shirye-shiryen ci gaba masu dorewa da za su tabbatar da walwalar dukkanin mazauna jihar.
A cewar gwamman:
"Manufarmu ita ce tabbatar da cewa an yi amfani da albarkatu da goyon bayan gwamnatin tarayya ta yadda ya kamata wajen ci gaban Sokoto."
Gwamna Ahmad ya yi fatan cewa wannan hadin guiwar zai kawo canje-canje masu amfani ga al'ummar jihar Sokoto.
Lakurawa sun fara ta'addanci a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa sabuwar kungiyar 'yan ta'addar Lakurawa sun fara ƙarfi a kananan hukumomi biyar a Sokoto inda a yanzu suka fara karbar Zakkah.
An ce kananan hukumomin da yan ta'addan suka mamaye sun hada da Tangaza da Illela da Gada da Binji da Silame kuma suna hukunta duk wanda ya saba masu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng