Sokoto: Kazamar Fada Ta Barke Tsakanin Turji da Sojoji, bayan Ganawa da Basarake
- Mun samu rahotanni da ke tabbatar da cewa ana kazamar fada tsakanin Bello Turji da dakarun sojoji a jihar Sokoto
- Sojojin da yan Gatawa sun kaure da yan ta'addan karkarshin jagorancin Bello Turji da safiyar yau Talata a Sokoto
- An tabbatar da an fara fadan tun misalin karfe 6.00 na safe, ana cigaba da fafatawa har zuwa lokacin tattara rahoton
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Rahotanni sun tabbatar da barkewar fada tsakanin sojoji da yan ta'adda a jihar Sokoto.
An tabbatar cewa ana fadan ne tsakanin sojoji da taimakon yan garin Gatawa da kuma yan ta'adda karkashin jagorancin Bello Turji.
Fada ya kaure tsakanin Bello Turji da sojoji
Shafin Zagazola Makama ya wallafa hakan da safiyar yau Talata 12 ga watan Nuwambar 2024 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya tabbatar da cewa an kaure ne tsakanin Bello Turji da sojojin da misalin karfe 6.00 na safiyar yau Talata.
Rahoton ya tabbatar da cewa har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ana cigaba da artabu a Bakin Gulbi kusa da Tungar Yakubu.
Turji ya gana da basarake a Sokoto
Kafin wannan farmaki na Bello Turji, dan ta'addan ya yi wata ganawar sirri da dagacin kauyen Dan Tasakko kusa da Gatawa a daren jiya Talata 12 ga watan Nuwambar 2024.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa an gudanar da ganawar da wasu kasurguman yan bindiga a bangaren Bello Turji, cewar Daily Post.
Ganawar ta jefa tsoro ga mazauna yankin kamar yadda suka tabbatar da cewa za a iya samun barazanar tsaro.
Yadda Bello Turji ke sheke ayarsa a Sokoto
A baya, kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa dan ta'adda, Bello Turji shi ke iko da mafi yawan ƙauyuka a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.
Shugaban karamar hukumar Isa, Alhaji Sharifu Kamarawa shi ya tabbatar da haka ga ƙaramin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Kamarawa ya ce dan ta'addan shi ke saukewa da kuma nada wasu daga cikin dagatai a mafi yawan ƙauyuka a jihar ta Sokoto.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng