Atiku Abubakar Ya Kafe a kan Bakarsa, Ya Sake Tunzura Gwamnatin Tinubu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali kan ceto yan Najeriya
- Wannan wani bangare ne na musayar yawu da ke giftawa tsakanin Atiku da gwamnatin tarayya kan ayyukan shugaban kasar
- Atiku Abubakar ya kara nanata matsayarsa kan yadda manufofin Tinubu ke kashe yan Najeriya a maimakon ceto su daga wahala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sake sako gwamnatin Bola Tinubu a gaba kan manufofin da ya ce su na kashe yan Najeriya.
Atiku Abubakar wanda ke daga cikin manyan yan adawa da gwamnatin APC mai mulki ya na ganin gwamnatin tarayya ta saki hanyar kawo ayyukan cigaba ga jama’a.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mataimakin Atiku Abubakar na musamman kan yada labarai, Phrank Sha'aibu ne ya yi martani ga gwamnatin tarayya bisa zargin maigidansa da yi wa Tinubu hassada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da rashin alkibla, ya ce har yanzu Tinubu ya gaza magance matsalolin kasar nan.
Sanarwar da hadimin Atiku ya fitar ta nuna cewa duk da cewa gwamnatin Tinubu ta yi kusan shekaru biyu a ofis, babu wani abin a zo a gani da ta yi wa yan kasa.
Atiku ya yi fatali da manufofin Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yan kasar ba su ga amfanin manufofin gwamnatin tarayya da APC ke jagoranta ba.
Ya bayyana takaicin yadda yan kasa ke mutuwa a cikin wahala, tare da ba gwamnati shawarar ta mayar da hankali a kan ayyuka na gari ba martani ga yan adawa ba.
Tinubu: Gwamnati ta zargi Atiku da hassada
A baya mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta soki yadda tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da yi wa shugaba mai ci, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu hassada.
Gwamnatin tarayya ta kara da cewa manufofin shugaban kasa sun fara saita kasar nan a kan hanyar samun wadata da murmurewar tattalin arziki, ba kamar yadda Atiku ke fadi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng