An Sake Gabatar da Bukatar Maido Tallafin Man Fetur ga Tinubu
- Wata kungiyar Arewa ta tsakiya ta sake tunkarar shugaban kasa Bola Tinubu kan maganar maido tallafin man fetur da ya cire
- MBF ta ce babu buƙatar dogon nazari domin fahimtar illar da cire tallafin mai ya yi wa tattalin arzikin Najeriya cikin watanni 17
- Shugaban kungiyar, Dr Bitrus Pogu ya ce suna fata Bola Tinubu zai kara nazari domin canza ra'ayi bayan jefa yan Najeriya a matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Kungiyar cigaban Arewa ta Tsakiya (MBF) ta yi kira na musamman ga Bola Ahmed Tinubu kan tsare tsaren tattali da ya kawo.
Kungiyar MBF ta ce a halin da ake ciki tattalin yan Najeriya ya ruguje kuma suna bukatar samun tallafi daga gwamnati.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa shugaban MBF, Dr Bitrus Pogu ne ya yi kira ga shugaban kasar a madadin kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar MBF ta bukaci maido tallafin mai
Shugaban kungiyar MBF, Dr Bitrus Pogu ya yi kira ga Bola Tinubu kan duba yiwuwar maido tallafin man fetur.
Dr Bitrus Pogu ya kara da cewa ya kamata shugaban kasar ya sake nazari kan karya darajar Naira da ya yi.
A cewar Dr Bitrus Pogu, matakai biyun da Bola Tinubu ya dauka sun jefa Najeriya a matsala inda miliyoyin mutane suka fada cikin mugun talauci.
MBF ta yi magana kan motocin CNG
Kungiyar MBF ta ce matakin samar da motocin CNG bayan cire tallafin mai abu ne mai kyau sai dai bai zo a kan gaɓa ba.
Sahara Reporters ta wallafa cewa Dr Bitrus Pogu ya ce ya kamata a fara samar da motoci da gidajen man CNG kafin a fara maganar cire tallafin fetur.
"Sai bayan ruguza tattalin arzikin Najeriya da sama da shekara aka fara maganar kawo motocin CNG.
Muna fatan Bola Tinubu zai kara nazari a kan matakin da ya dauka na cire tallafin mai domin saukakawa al'umma."
- Dr Bitrus Pogu, shugaban MDF
Tinubu ya yi martani ga Atiku Abubakar
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi martani ga Atiku Abubakar kan yawan sukansa da ya yi.
Fadar shugaban kasa ta ce akwai alamun Atiku Abubakar yana yi wa Bola Tinubu hassada a kan mulkin da ya samu a shekarar 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng