Dan NNPP Ya Saɓawa Gwamnonin Arewa, Zai Marawa Kudurin Haraji Baya a Majalisa

Dan NNPP Ya Saɓawa Gwamnonin Arewa, Zai Marawa Kudurin Haraji Baya a Majalisa

  • Dan majalisar Kano mai wakiltar Kiru/Bebeji, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayya goyon baya ga sabon kudurin Tinubu
  • Ya ce ya na da tabbacin majalisa za ta marawa kudurin haraji da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke kokarin aikawa masu baya
  • Wannan na zuwa a matsayin martani ga shirin wasu yan majalisa na hade kan wakilan Arewa wajen fatali da kudurin harajin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Dan majalisa AbdulMumin Jibrin Kofa ya bijirewa takwarorinsa na Arewa kan sabon kudurin haraji da shugaba Bola Tinubu ya bijiro da shi.

Gwamnonin Arewa da yan majalisa irinsu Sanata Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya ce idan aka tabbatar da sabon kudurin, hakan zai yi wa tattalin arzikin kasa illa matuka.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

Hon. AbdulMumin
Hon. Kofa ya goyi bayan kudurin harajin Tinubu Hoto: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa amma a bayaninsa, dan majalisa mai wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, AbdulMumin Jibrin Kofa ya ce ya gamsu da kudurin harajin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisar Kano ya goyi bayan kudurin haraji

Channels Television ta wallafa cewa dan majalisar wakilai, Hon. AbdulMumin Jibrin ya ce ba dukkanin jagororin Arewa ne ke adawa da kuduri harajin Tinubu ba.

Ya bayyana cewa ya na da yakinin yan majalisa za su amince da kudurin harajin da zarar Bola Tinubu ya aikawa majalisa.

Dan majalisa zai ingaza kudurin harajin Tinubu

Dan majalisa, Hon. AbdulMumun Jibrin Kofa ya bayyana cewa zai goyi bayan sabon kudurin haraji da wasu daga cikin jagororin Arewa ke adawa da shi.

Hon. Jibrin Kofa ya kara da cewa da zarar an zartar da kudurin ya zama doka, yan Najeriya za su gane cewa ba shi da wani nakasu ga Arewa ko kasar nan.

Kara karanta wannan

Sanata ya ga halin da talakawa ke ciki, ya nemi mafita daga shugaba Tinubu

Tinubu: Dan majalisa ya soki kudurin haraji

A baya kun ji cewa dan majalisa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ba za su rika kallon gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta na kara wahalar da talakawa ba.

Sanata Ali Ndume ya nuna adawa da sabon kudurin, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan shirin kara harajin VAT a shekarar 2025 ba, domin a ganinsa zai kara matsin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.