Lakurawa Sun Gano Hanyar Daukar Matasa cikin Sauki, Ta'addanci Zai Ƙaru

Lakurawa Sun Gano Hanyar Daukar Matasa cikin Sauki, Ta'addanci Zai Ƙaru

  • Yan kungiyar Lakurawa sun fara daukar matasa a jihar Sakkwato domin shigar da su cikin sabuwar tafiyar ta'addanci
  • An fara koke da bullar sabuwar kungiyar a jihohin Kebbi da Sakkwato da ke fama da ayyukan yan bindiga a halin da ake ciki
  • Sabuwar kungiyar, mai ra'ayi irin na Boko Haram ta fara daukar matasa ta hanyar ba su kudi da yi masu huduba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - An samu matsala a Sakkwato bayan yan ta'addan Lakurawa sun gano lagon daukar wasu daga cikin matasan jihar a matsayin sababbin yan ta'adda. A yan kwanakin nan ne jami'an tsaron Najeriya su ka tabbatar da bullar yan ta'addan a jihohin Kebbi da Sakkwato, kuma sun samo asali ne daga Mali da Nijar.

Kara karanta wannan

Amnesty Int'l ta caccaki gwamna bisa zargin jikkata yar gwagwarmaya

Sakkwato
Lakurawa sun fara daukar sababbin yan ta'adda Hoto: @ZagazOlaMakama/Fatima Ahmed Aliyu
Asali: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa wani bidiyo a shafinsu na X da ke nuna yadda yan ta'addan ke tara jama'a a kauyuka su na shigar da su muguwar kungiyarsu.

Sakkwato: Hanyoyin daukar yan ta'addan Lakurawa

An gano yadda yan ta'addan Lakurawa su ke amfani da tsatstsauran ra'ayi irin na Boko Haram wajen jan ra'ayin matasa domin su shiga cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma Lakurawan na tara matasa su na basu kudi masu tarin yawa domin su rungumi ra'ayin da su ka zo da shi, musamman a Sakkwato.

Lakurawa sun fatattaki masu garkuwa da mutane

Wasu daga cikin yan kungiyar Lakurawa sun kori yan bindiga da su ka addabi sassan Arewa maso Yamma.

An ruwaito cewa sun kuma kori yan bindiga daga yankunan da su ka mamaye tare da kwace dukkanin shanun da su ka mallaka.

Lakurawa sun fara tattara zakka a Sakkwato

A baya mun wallafa cewa yan kungiyar Lakurawa sun fara nuna abin da su ka zo da shi bayan sun tilastawa jama'a biyan zakka da sanya masu dokoki masu tsauri.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun yi karfi a Sokoto, suna karbar zakka, sun yiwa al'umma gargadi mai tsauri

Shugaban karamar hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni ne ya tabbatar da lamarin, inda ya kara da cewa sun fara kwace dukiyoyin jama'a ta karfin tsiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.