'Ku Tsaya Gida, Ku Bar Fita Kasar Waje,' Tinubu Ya Aika Sako ga Matasa Masu Digiri
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ja hankalin matasan Najeriya da su yi amfani da ilimi wajen kawo ci gaba a ƙasar nan
- Tinubu ya kuma shawarci matasa da su guji fita waje, su maida hankali kan inganta Najeriya tare da kawo cigaba a cikin gida
- Shugaban kasar ya nanata cewa gwamnati ta saka jari a ilimin matasan kuma yana fata su taimaka wajen kawo babban sauyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Uyo - Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga matasa masu digiri a Najeriya da su yi amfani da iliminsu domin inganta al’umma da ci gaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi wannan kiran ne a lokacin bikin yaye dalibai karo na 29 da 30 na Jami’ar Uyo (UNIUYO) a ranar Asabar.
Jaridar Vanguard ta rahoto Tinubu ya shawarci waɗanda suka kammala karatu da kada su yi gaggawar fita ƙasashen waje neman kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya roki matasa su tsaya gida
Tinubu ya roki matasan da su tsaya cikin kasar su ginata domin kawo habakar arzikinsu da na kasar baki daya.
Tinubu ya bayyana cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban ƙasa kuma ya kamata ya zama na zamani wanda ke da sauƙin fahimta ga dalibai.
“Gwamnati ta saka jari sosai a iliminku, don haka muna fatan zaku taka rawar gani wajen ciyar da ƙasa gaba.”
- A cewar Tinubi.
Yayin da matasan ke shirin shiga cikin al'umma domin gogayya a neman aiki ko sana'a, ya nemi su kasance abin kwatance ta hanyar amfani da basirarsu.
“Kada ku fara yin tunanin fita ƙasasashen waje neman abin duniya; a tare, za mu iya samar da wani yanayin samun kudi mai kyau a Najeriya.”
- A cewar shugaban kasar.
Tinubu ya roki 'yan Najeriya kan tattali
Da ya samu wakilacin shugaban jami’ar Fatakwal, Farfesa Owunari Georgewill, Tinubu ya koka kan yadda ba ayin amfani da binciken dalibai wajen kawo sauyi.
Ya lura da cewa, duk da ƙalubalen da ake fuskanta, gwamnati ta himmatu wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan.
“Ina roƙon ‘yan Najeriya su kara goyawa gwamnati baya kan manufofin sauyin tattalin arziki, duk da ƙalubalen da manufofin za su iya kawo wa."
- Inji Tinubu.
Asali: Legit.ng