'Ka Hana Wike, Gwamnoni ba Alkalai Motoci da Gidaje,' SERAP Ta Fadawa Tinubu
- SERAP ta nemi shugaban kasa Tinubu ya dakatar da bayar da mota da gidaje ga alkalai, tana jaddada rashin dacewar hakan
- Kungiyar ta yi zargin cewa ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnoni ne ke shirin ba alkalai kyautar gidaje da motocin
- SERAP ta roki ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya kalubalanci sahihancin ba da wadannan kyaututtuka ga alkalai a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar SERAP ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da ministan Abuja da gwamnonin jihohi daga nuna iko kan fannin shari’a.
SERAP ta nuna damuwa kan shirin Nyesom Wike da gwamnonin na bayar da kyautar motoci da gidaje ga alkalai, tana gargadin cewa hakan zai nakasa fannin.
SERAP ta aika wasika ga Shugaba Tinubu
Kungiyar ta roki Tinubu da ya umarci ministan shari’a ya kalubalanci sahihancin dokar yin irin wannan kyauta a kotu, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasikar da ta rubuta a ranar 9 ga Nuwamba, wadda Kolawole Oluwadare ya sanya hannu, SERAP ta jaddada muhimmancin kare martabar fannin shari’a.
SERAP ta ce dole ne fannin shari’a ya tsaya da kafafunsa, ba tare da tasiri daga bangaren gwamnati ko majalisa ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
SERAP ta nemi a kare martabar shari'a
Kungiyar ta gargadi cewa yin katsalandan a harkokin shari’a zai iya rage rawar da shari’a ke takawa wajen yin hukunci ga mahukuntan gwamnati.
Wasikar SERAP ta bukaci gwamnati da ta inganta kudaden fannin shari’a da yanayin aikinta domin kare fannin daga tasirin gwamnati ko jami'anta.
SERAP ta jaddada cewa akwai alhakin kare martabar fannin shari'a da ya rataya kan Najeriya wanda ke da muhimmanci wajen samun yardar jama’a.
SERAP ta yi barazanar zuwa kotu
Kungiyar ta bukaci a dauki mataki kan lamarin cikin kwanaki 7, tana gargaɗin daukar matakan shari’a idan ba a samu amsa ba daga gwamnati.
Rahotanni na cewa ba da kyautar mota da gidaje ga alkalai ba tare da bin hanyoyin doka ba, na iya yin illa ga doka da kuma fannin shari'ar kasar nan.
SERAP ta bukaci gwamnati ta dakatar da wannan dabi’a, ta kuma tabbatar da cewa shari’a tana aiki ba tare da katsalandan daga gwamnati ba.
SERAP ta kai koken gwamnoni ga Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa SERAP ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu, da ya binciki yadda gwamnoni da ministan Abuja suka kashe bashin da suka karɓo daga bankin duniya.
SERAP ta buƙaci Tinubu ya umarci ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) da hukumomin yaƙi da rashawa da su gaggauta bincikar yadda aka kashe bashin na $1.5bn.
Asali: Legit.ng