'Zan Kawo Kano': Yusuf Ata Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Tinubu na Nada Shi Minista
- Sabon karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya ce burinsa shi ne dawo da Kano ga jam'iyyar APC a 2027
- Yayin ziyararsa ta farko a Kano bayan rantsar da shi, Yusuf Ata ya bayyana cewa nadinsa na da muhimmanci wajen karfafa APC
- Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, inda ya jaddada kudurinsa na ciyar da APC gaba a Kano ta hanyar ziyartar jihar duk da tarin aikinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Sabon ministan ma'aikatar gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana burinsa na dawo da jihar Kano ga jam'iyyar APC a 2027.
Yusuf Ata ya bayyana hakan ne a lokacin ziyararsa ta farko zuwa Kano bayan rantsar da shi a majalisar ministoci ta tarayya.
Yusuf ya fadi dalilin nadasa minista
Ministan ya bayyana cewa nadinsa yana da alaka da siyasa, yana mai cewa ya zama dole APC ta karbi jihar Kano, musamman a Kano ta Tsakiya, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Ata ya tabbatar da cewa zai kasance yana ziyartar mazabarsa a Kano duk da aikinsa na minista domin tabbatar da nasarar jam'iyyar APC.
Duk da matsayinsa na minista, Yusuf Ata ya dauki alkawari cewa zai mayar da hankali wajen samun nasarar siyasa a Kano kafin zaben 2027.
Minista ya ci burin farantawa Tinubu
Ya godewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda nadin, yana mai cewa an yi hakan ne domin al’ummar Kano da Najeriya.
Ata ya yi alkawarin dawo da jihar Kano ga APC a 2027, yana mai nuna jajircewarsa ga nasarar jam’iyyar.
“Wannan shi ne tabbacin da na bai wa shugaban kasar,” a cewar Yusuf Ata yayin da yake nuna yakininsa wajen cimma wannan manufa.
'Dalilin Tinubu na tsige ni minista' - T Gwarzo
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon ƙaramin ministan harkokin gidaje da raya birane, Abdullahi T. Gwarzo ya ce babu laifin da ya yi aka sauke shi daga muƙamin.
Ya ce dalilin sauke shi daga matsayin minista shi ne yankin da ya fito watau Kano ta Arewa na da mutane masu muƙamai da yawa a gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng