Bidiyo: NDLEA Ta Cafke Kwayoyi a Buhunan Gyada, An Gano Kasar da Za a Kai Su
- Hukumar NDLEA ta dakile kokarin safarar miyagun kwayoyi zuwa Birtaniya, inda aka gano su cikin huhun gyada da na aya
- Femi Babafemi, daraktan labaran NDLEA, ya gargadi jama'a akan karɓar kaya ba tare da sun duba abin da ke a cikinsu ba
- A cikin wani faifan bidiyo da Babafemi ya wallafa a shafin hukumar, an ga jami'an NDLEA lokacin da suka gano kwayoyin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Hukumar NDLEA ta dakile yunƙurin fitar da miyagun kwayoyi zuwa Biritaniya ta hanyar gano su cikin buhunan gyada da aya.
Shugaban Sashen Harkokin Jarida na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana wannan a cikin bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta.
NDLEA ta cafke kwayoyi a filin
A cikin bidiyon da aka wallafa a intanet, an ga jami’an hukumar suna bincikar buhunan, inda aka gano miyagun kwayoyi da aka ɓoye a ciki, inji Vanguad.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce an yi nufin safarar miyagun kwayoyin zuwa kasar Biritaniya.
Femi Babafemi ya gargadi jama’a da su guji karɓar kaya ba tare da duba abin da ke ciki ba. Ya ce yana da muhimmanci a duba kaya sosai.
An boye kwayoyi a buhun aya da gyada
Femi Babafemi ya bayyana cewa:
“Kada ku karɓi kowanne kaya ba tare da duba abin da ke ciki ba, ko da kuwa babu wata alamar laifi a tare da kayan."
Bidiyon da Babafemi ya raba ya nuna yadda jami’an NDLEA suka gano miyagun kwayoyi a cikin buhunan aya da gyada wanda hakan ya ƙara tabbatar da wannan gargaɗin.
Hukumar ta NDLEA ta dakile wannan babban yunƙuri na fitar da miyagun kwayoyi zuwa Biritaniya, wanda ya nuna jajircewar jami'anta wajen dakile safarar kwayoyi.
Kalli bidiyon a kasa:
An zargi jami'an NDLEA da kashe matashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa An zargi wasu jami’an hukumar NDLEA da kashe wani matashi mai suna Faisal Yakubu Hussaini.
Ana zargin jami’an na NDLEA sun kashe Faisal Yakubu ne a garin Dangi, hedikwatar karamar hukumar Kanam a jihar Filato a wani samame.
Asali: Legit.ng