Bullar 'Yan Ta'addan Lakurawa: Mukaddashin Hafsun Sojoji Ya Isa Jihar Sokoto

Bullar 'Yan Ta'addan Lakurawa: Mukaddashin Hafsun Sojoji Ya Isa Jihar Sokoto

  • Muƙaddashin babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya isa jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya isa jihar Sokoto ne domin ziyarar aiki ta farko a rundunar shiyya ta takwas
  • Ziyarar muƙaddashin COAS ɗin na zuwa ne bayan an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ƴan ta'adda mai suna Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Muƙaddashin babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya (COAS) Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya isa Sokoto domin gudanar da ziyarar aiki ta farko a rundunar shiyya ta takwas.

A jihar Sokoto ta yankin Arewa-maso-Yamma, ana sa ran zai ziyarci Sarkin Musulmi, Mai alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin sojojin sama sun soye 'yan ta'addan ISWAP masu yawa a Borno

Mukaddashin COAS ya isa Sokoto
Mukaddashin COAS ya kai ziyarar aiki a Sokoto Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Muƙaddashin COAS ya je Sokoto

Tashar Channels tv rahoto cewa Laftanar Olufemi Oluyede zai gana da sauran masu ruwa da tsaki a rundunar shiyya ta takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muƙaddashin COAS ɗin zai yi amfani da ziyarar wajen yin jawabi ga dakarun Operation Fasan Yamma da ke yaƙi da ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Ƴan ta'adda sun ɓulla a Sokoto da Kebbi

Ziyarar Oluyede na zuwa ne kwanaki uku bayan hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta tabbatar da ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci da aka fi sani da ‘Lakurawa’ a jihohin Sokoto da Kebbi.

Ƙananan hukumomi biyar na jihar Sokoto na fuskantar ƙalubale daga sabuwar ƙungiyar ta'addancin wacce aka fi sani da Lakurawa.

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce sabuwar ƙungiyar ƴan ta’addan na ƙara ta’azzara rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma amma rundunar sojojin Najeriya na fafatawa da su.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun tunkari mayakan sabuwar ƙungiyar ƴan ta'adda, an rasa rayuka

Ta'addancin ƙungiyar Lakurawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mazauna jihar Sokoto sun bayyana yadda sabuwar kungiyar ta'addanci ta Lakurawa ke mu'amalantarsu.

An bayyana cewa Lakurawa na jingina da addini kuma suna yin horo na musamman ga duk wanda ya karya dokar da suke gani ta addini ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng