Kwankwaso Ya Taya Trump Murnar Lashe Zabe, Ya Fadi Abin da Nasarar Ta Tuna Masa

Kwankwaso Ya Taya Trump Murnar Lashe Zabe, Ya Fadi Abin da Nasarar Ta Tuna Masa

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya bi sahun masu taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka murnar nasarar da ya samu a zaɓe
  • Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa dawowar Trump kan mulki abu ne wanda za a yi nazarinsa nan da shekaru masu zuwa
  • Kwankwaso ya nuna cewa nasarar Trump ta tuna masa da lokacin da ya sake dawowa kan madafun ikon Kano bayan ya yi rashin nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, murnar nasarar da ya samu a zaɓe.

Saƙon taya murnar na Kwankwaso na zuwa ne bayan Donald Trump ya yi nasara kan Kamala Harris a zaɓen shugaban ƙasan Amurka.

Kara karanta wannan

TCN: Ƴan Najeriya za su ɗauki lokaci ba wutar lantarki, an gano matsaloli 3 a Arewa

Kwankwaso ya taya Trump murna
Kwankwaso ya Trump murnar lashe zabe Hoto: @realDonaldTrump, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kwankwaso ya taya Trump murna

Kwankwaso ya taya Donald Trump murnar nasarar da ya samu ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa sake komawar Trump kan madafun iko wani abu ne da za a riƙa yin nazari a kansa a shekaru masu zuwa.

Me nasarar Trump ta tunawa Kwankwaso?

Kwankwaso ya ce nasarar Trump ta tuna masa da lokacin da ya sake komawa kan mulkin jihar Kano bayan shekara takwas.

"Ina miƙa sakon taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Donald Trump da tawagarsa, kan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar Amurka da aka gudanar kwanan nan."
"Wannan nasara ta tuna min da irin gogewar da na samu a shekarar 2011 lokacin da ni ma na taka rawar gani a siyasance na lashe zaɓen gwamna a jihar Kano, bayan da na faɗi zaɓe shekaru takwas da suka gabata ina gwamna.

Kara karanta wannan

"Ana tunzura ni in yi wa Kwankwaso butulci" Inji Abba Gida Gida

"Irin wannan dawowar ta siyasa tana buƙatar sadaukarwa, jajircewa, aiki tuƙuru, juriya, da ƙaƙƙarfan ƙauna da goyon baya daga mutanen ka."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya kuma yabawa shugaban ƙasa mai barin gado, Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris, kan tabbatar da an yi sahihin zaɓe tare da amincewa da nasarar jam'iyyar Republican.

Trump ya fara naɗi a gwamnatinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa zaɓaɓɓen shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi nadin farko a gwamnatin da za ta karbi ta Joe Biden nan da wasu watanni masu zuwa.

Trump ya nada Susie Wiles a matsayin shugabar ma'aikatan fadarsa ta White House, ita ce mace ta farko da ta rike mukamin a tarihin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng