Jigo Ya Tsallake Kwankwaso, Atiku, Ya Fadi Wanda Zai Karbi Mulki Hannun Tinubu

Jigo Ya Tsallake Kwankwaso, Atiku, Ya Fadi Wanda Zai Karbi Mulki Hannun Tinubu

  • Yunusa Tanko, shugaban kungiyar "Obidient Movement," ya nuna cewa Peter Obi zai iya zama shugaban Najeriya a 2027
  • Tanko ya ce rashin nasarar Obi a 2023 ya faru ne sakamakon zamba a zabe, inda ya ce ba za a sake maimaita irin haka ba
  • Shugaban 'yan Obidient ya yi kira da a gyaran tsarin zabe da kuma samun haɗin kai domin kawo canji mai ma'ana a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambara - Yunusa Tanko, shugaban kungiyar "Obidient Movement," na kasa ya tabbatar da cewa Peter Obi zai iya zama shugaban Najeriya a zaben 2027.

Tanko ya danganta rashin nasarar Obi a 2023 da zargin zamba a zabe, yana ganin "sabuwar Najeriya" zata yiwu idan an zabi shugabanni na gaskiya.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da Tinubu ya isa birnin Riyadh, zai halarci manyan tarurruka 2

Tanko Yunusa ya yi magana kan yiwuwar nasarar Peter Obi a zaben 2027.
Tanko ya dora yakinin cewa Peter Obi zai iya lashe zaben shugaban kasa a 2027. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

'Peter Obi zai lashe zaben 2027' - Tanko

Jaridar Punch ta rahoto Tanko ya yi maganar ne a wani taron da aka yi a Onitsha, jihar Anambra, wanda aka tsara kan sabunta tafiyar 'yan 'Obidient.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kungiyar ta mai da hankali wajen samar da shugabanci mai kyau, da kuma haɗin kai, adalci da gaskiya ta hanyar haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki.

Tanko yana ganin Obi zai iya zama shugaban ƙasa a 2027 idan aka shirya wakilan zabe da kyau kafin babban zaben 2027 mai zuwa.

Tanko ya nemi a gyara tsarin zabe

Ya jaddada cewa zabar shugabanni na gaskiya shi ne hanya mafi kyau ta samar da "sabuwar Najeriya" da kuma kawo ƙarshen mugun shugabanci.

Tanko ya tabbatar da cewa Obi ne ya lashe zaben 2023, amma aka hana shi nasara saboda zamba, inda ya ce ba za a maimaita wannan tarihi ba.

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, yan APC sun watsawa Gwamna kasa a ido, sun goyi bayan dan adawa

Ya yi kira da a gyaran tsarin zabe, ta hanyar karfafa dokokin zaben da kuma tabbatar da adalci a zaben yayin da kuma ya ƙarfafi matasa kan samar da canji mai ma'ana.

Hadakar Kwankwaso da Obi ta yi karfi

A wani labarin, mun ruwaito cewa maganar haɗaka tsakanin Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi a kan zaben shekarar 2027 ta fara yin karfi.

Bayan bayanin da Sanata Kwankwaso ya yi kan yiwuwar haɗakar, jam'iyyar LP ta yi maratanin cewa ta yi na'am da abin da ya fada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.