'Shugabanni Su Gaggauta Daukar Mataki,' Kwankwaso Ya Lissafa Matsalolin Najeriya
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce Najeriya na fuskantar rashin tsaro, matsalar tattalin arziki, da rashin ababen more rayuwa
- Kwankwaso ya ce akwai bukatar shugabanni su fi mayar da hankali wajen yiwa al'umma aiki ba wai neman ribar siyasa ba
- Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana damuwarsa kan matsalar rashin tsaro da ake fuskanta musamman a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a 2023, ya bukaci shugabanni su yi aiki tukuru domin gyara matsalolin Najeriya.
Kwankwaso ya lissafa rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da kuma ƙarancin ababen more rayuwa, musamman wutar lantarki, a matsayin manyan matsaloli.
Jagoran Kwankwasiyyar ya bayyana hakan ne a Nvosi, jihar Abia, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya bayyana matsalolin Najeriya
Jaridar ta ce Kwankwaso ya ziyarci Abia ne domin yin ta’aziya ga Gwamna Alex Otti na rasuwar gwamnan farko na jihar, Dakta Ogbonnaya Onu.
Kwankwaso ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, kuma dole shugabanni su dauki matakan magance su, musamman wutar lantarki.
"Kowa ya gane cewa muna da manyan matsaloli; rashin tsaro, kalubalen tattalin arziki da kuma ƙarancin ababen more rayuwa, musamman wutar lantarki."
- A cewar Kwankwaso.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce yin abin da ya dace shi ne mabuɗin nasara a siyasa, yayin da bin son zuciya zai iya jawo fushi daga al'umma.
Kwankwaso ya ba shugabanni shawara
Kwankwaso ya lura cewa yin aiki mai kyau ya zarce shirin neman tazarce, yana mai cewa shugabanci yana nufin hidima ga jama'a, ba kawai neman ribar siyasa ba.
Ya tunatar da ‘yan siyasa cewa shugaba na iya rasa zabe, yana kawo misali daga faduwarsa a 2003 da kuma rashin nasarar Jonathan a 2015.
A kan rashin tsaro, Kwankwaso ya bayyana rashin tsaro da ake ciki a Arewa, inda al’umma ke fuskantar barazana daga ‘yan bindiga, har suna biyan haraji gare su.
Hanyar dawo da zaman lafiya - Kwankwaso
A wani labarin, mun ruwaito cewa jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce sojoji za su iya kawo karshen kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Kwankwaso ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya za ta iya kawar da wannan matsala ta tsaro gaba ɗaya matuƙar ta samu kwarin guiwar da ya dace.
Asali: Legit.ng