‘Akwai Kulli’: An Zargi Wasu da Kisan Lagbaja, an Shawarci Tinubu kan Gawarsa
- Yan gargajiya a kauyen Ilobu da ke karamar hukumar Irepodun sun fara nemo hanyar daukar matakai kan mutuwar Taoreed Lagbaja
- Mazauna yankin na cigaba da alhinin mutuwarsa inda suke zargin ba mutuwar Allah da annabi Lagbaja ya yi ba
- Hakan na zuwa ne bayan mutuwar hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja a jihar Lagos bayan fama da jinya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Zarge-zarge na cigaba da bullukowa kan mutuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagabaja.
Wasu yan gargajiya a jihar Osun sun yi zargin cewa ba haka kawai Lagbaja ya mutu ba akwai wani abu a kasa.
Ana zargin kashe Taoreed Lagbaja aka yi
Yayin hira da Tribune, dan gargajiya, Awopegba Ifagbemi ya ce yan yankin da Lagbaja ya fito na cigaba da jimamin rasuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ifagbemi ya ce ba mutuwar Allah da annabi Lagabaja ya yi ba akwai wasu zarge-zarge kan rasuwarsa da ya yi ba zato.
Daga bisani Ifagbemi ya roki Gwamnatin Tarayya ta mika gawar Taoreed Lagbaja domin yin bincike ta hanyar tsatsube-tsatsube.
Ya ce yan gargajiya a yankin Ilobu a karamar hukumar Irepodun sun yi ganawa game da lamarin domin nemo hanyar shawo kan matsalar.
Al'umma sun yi jimamin mutuwar Lagbaja
Wani shugaban kauyen mai suna, Alhaji Dauda Taofeek ya ce mutuwar Lagbaja ba karamin rashi suka yi ba a yankin.
Taofeek shi ma ya tabbatar da cewa ba haka banza Lagbaja ya mutu ba kuma wadanda suka yi ajalinsa sai sun dandana kudarsu.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawan wuraren kasuwanci da marigayin ya bude an rurrufe su.
Baffan marigayi Lagbaja ya yi nadama
A baya, kun ji cewa an zargi mutuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja kan rigimar filaye da ake yi a jihar Osun.
Baffan marigayin mai suna Tajudden Lagbaja ya ce ya yi nadamar nema masa fom na NDA a shekarun baya.
Hakan na zuwa ne bayan rasuwar hafsan sojojin Najeriya a jihar Legas bayan fama da jinya wanda har an nada mukaddashinsa.
Asali: Legit.ng