Yadda Dakarun Sojojin Najeriya Suka Hallaka 'Yan Ta'adda 169
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana irin nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan ƴan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya
- DHQ ta bayyana cewa dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 169 tare da cafke wasu mutum 641 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban
- A cikin sanarwar da daraktan yada labarai na DHQ ya fitar, ya ce 70 daga cikin ƴan ta'addan an kashe su ne a jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce sojojin da aka tura domin yaƙi da ta'addanci sun hallaka ƴan ta'adda 169 tare da cafke mutane aƙalla 641 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
DHQ ta ƙara da cewa an kashe 70 daga cikin ƴan ta’addan a Kwallaram da ke jihar Borno ta hanyar kai hare-hare ta sama.
Sanarwar da daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Buba Edward ya fitar ta kuma ce an fatattaki ƴan ta’adda da dama daga maboyarsu, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka hallaka ƴan ta'adda
Edward Buba ya bayyana cewa hare-haren da sojojin sama da farmakin da sojojin ƙasa ke kaiwa ya sanya an fatattaki ƴan ta'adda daga maɓoyarsu inda aka kashe da dama daga cikinsu.
"Misali, a ranar 6 ga watan Nuwamba, dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai sun kai farmaki ta sama kan ƴan ta’addan da ke tsibirin Kwallaram da Arianna Ciki a jihar Borno."
"Harin ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta’adda sama da 70 a Kwallaram, tare da kashe wasu da dama a Arianna Ciki. A cikin makon da ake bitar, sojoji sun kashe ƴan ta'adda 169 tare da cafke mutane 641."
- Manjo Janar Edward Buba
Sojoji sun cafke ɓarayin mai
Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa, a yayin da ake gudanar da aikin yaƙi da satar man fetur, an kama mutane 40 da ake zargin barayin mai ne, sannan an kwato ɗanyen mai da aka sace wanda kuɗinsa ya kai N1bn.
"Sojojin sun kuma kama mutum 40 da suka aikata laifin satar mai tare da kuɓutar da mutane 181 da aka yi garkuwa da su."
- Manjo Janar Edward Buba
Sojoji sun yi bajinta
Ashiru Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da sojojin suka samu abin a yaba ne domin sun yi ƙoƙari sosai.
"Gaskiya wannan nasara ce mai girma, muna yaba musu kan ƙoƙarin da suke yi wajen samar da tsaro a ƙasar nan."
"Muna fatan za su ci gaba da ƙoƙarin da suke yi na fatattakar ƴan ta'adda masu takurawa bayin Allah."
- Ashiru Kabir
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda sama da 400
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarori masu dumbin yawa a ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a sassan Najeriya a watan Oktoba da ya gabata.
Gwarazan sojoji a rundunoni daban-daban sun hallaka ƴan ta'adda 481 tare da cafke wasu 741 da ake zargi da aikata miyagun laifuka a wata ɗaya kacal.
Asali: Legit.ng