Bayan Ayyana Ilimi Kyauta, Gwamna a Arewa Ya Kawo Sabon Tsari a Manyan Makarantu

Bayan Ayyana Ilimi Kyauta, Gwamna a Arewa Ya Kawo Sabon Tsari a Manyan Makarantu

  • Gwamna Kefas Agbu na Taraba ya jaddada aniyar samar da ilimi mai inganci tare da kallon fikira a matsayin babbar kadara
  • Gwamnan ya kuma sanar da canja lokacin yaye dalibai a jihar tare da fatan Kwalejin Zing ta zamo cibiyar horas da malamai
  • Yayin da Kefas ya karfafi malaman kwalejin, ya kuma jaddada manufar gwamnatinsa na ba da ilimi kyauta da tilasta shi ga yara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya sake jaddada aniyarsa ta aiwatar da gyaran ilimi da zai ba 'yan jihar damar samun ingantaccen ilimi mai rahusa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye dalibai a Kwalejin Ilimi ta Zing da aka gudanar a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

‘Yan adawa sun fara yabawa a Kano, Abba ya yi bayanin yadda yake inganta lantarki

Gwamnan jihar Taraba ya yi magana kan sauya lokacin yaye daliban manyan makarantu
Gwamnan Taraba ya sauya lokacin yaye daliban manyan makarantun jihar. Hoto: @OfficialTaraba
Asali: Twitter

Gwamna ya tilasta ilimi a Taraba

Gwamna Kefas ya bayyana bikin yaye daliban a matsayin wani gagarumin nasara ga dukkanin waɗanda suka kammala karatu daga 1994 zuwa yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Kefas ya ce:

"Arziki na hakika ba wai ya ta'allaka ga albarkatun ƙasa da ci gaban tattalin arziƙi kaɗai ba; yana da alaka ne ga basirar tunani da ƙirƙire-ƙirƙiren al’ummar jihar."

A cewarsa gwamnan, ilimi shine tushen ci gaban gwamnatinsa, wanda ya sa gwamnatinsa ta ayyana ilimi kyauta da tilasta shi a matakin firamare da sakandare a fadin jihar.

Gwamna ya canja tsarin manyan makarantu

Gwamna Kefas ya bayyana Kwalejin Ilimi ta Zing a matsayin cibiyar horar da malamai a fadin jihar, inda ya ba da shawarar kafa kwamitin aiwatar da wannan tsari a kwalejin.

Gwamnan ya yabawa shugabancin kwalejin kan yadda suka dage wajen samun ci gaba a bangaren ilimi, yana mai jaddada rawar da ilimi ke takawa wajen ƙarfafa matasa.

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

Kefas ya sanar da cewa, daga yanzu, dukkan manyan makarantu a jihar za su rika gudanar da bikin yaye dalibai a kowace shekara.

Taraba - Gwamna ya ayyana ilimi kyauta

Tun da fari, mun ruwaito cewa Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya ya maida karatun makarantar Firamare da Sakandire kyauta a jihar.

Gwamna Kefas ya bayyana wannan kyakkyawan labari ga dalibai da iyaye yayin da ya kai ziyara makarantar Firamare da ke Wukari ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.