Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Dan Arewa a Shirgegen Mukami a Gwamnatinsa

Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Dan Arewa a Shirgegen Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake naɗa Darakta-Janar na hukumar NBRDA a wa'adi karo na biyu
  • Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Abdullahi Mustapha wanda ɗan asalin jihar Kano ne domin ci gaba da jan ragamar hukumar
  • Sanarwar sake naɗin Farfesa Abdullahi Mustapha na ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, George Akume

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sake yin naɗin muƙami a gwamnatinsa.

Shugaba Tinubu ya amince da sake naɗa Farfesa Abdullahi Mustapha a matsayin Darakta-Janar na hukumar NBRDA a karo na biyu.

Shugaba Tinubu ya yi nadi a gwamnatinsa
Shugaba Tinubu ya nada shugaban hukumar NBDRA Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abdullahi Mustapha
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Darakta-Janar na hukumar NBRDA, Toyin Omozuwa, ta fitar a Abuja ranar Asabar.

Kara karanta wannan

APC ta yi manyan kamu, tsohon ɗan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya sake naɗa Darakta-Janar na NBRDA

A cewar sanarwar, an sanar da naɗin Farfesa Abdullahi Mustapha ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

"Wa’adin Farfesa Abdullahi Mustapha na biyu ya fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Oktoba, 2024 kuma ya yi daidai da tanade-tanaden sashe na 10 (1) da (3) na dokar hukumar NBRDA."

- Toyin Omozuwa

Toyin Omozuwa ta bayyana cewa ƙwararru a fannin masana'antu na kallon sake naɗin Abdullahi Mustapha a matsayin ƙwarin gwiwar da Shugaba Tinubu ke da shi a kansa na samar da sababbin abubuwa don samun wadatar abinci.

Ta ƙara da cewa sake naɗin zai ba Abdullahi Mustapha damar kammala aikinsa na inganta samar da magunguna, tare da sanya Najeriya a sahun gaba wajen bunƙasa masana'antu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe naɗe a hukumar INEC ta ƙasa, an samu bayani

Abdullahi Mustapha Farfesa ne a fannin Bioinorganic Chemistry kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Dambatta ta jihar Kano ne.

Tinubu ya ba ɗan tsohon gwamna muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da nadin dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo mukami.

Tinubu ya nada Adebayo ne a matsayin shugaban hukumar ci gaban harkokin noma da aka fi sani da NALDA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng