Damfarar $3.3m: Gwamnati Ta Yi Magana kan Cafke Dan Siyasar Najeriya a Amurka

Damfarar $3.3m: Gwamnati Ta Yi Magana kan Cafke Dan Siyasar Najeriya a Amurka

  • Gwamnatin jihar Anambra ta ba za ta kare shugaban ƙaramar hukumar Ogbaru, Franklin Nwadiolo da ake cafke kan zargin damfarar $3.3m
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya bayyana cewa ba Gwamna Chukwuma Soƙudo ba ne ya naɗa shi muƙami a gwamnatinsa
  • Wani jigon jam'iyyar APGA a jihar Anambra ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar a mataimakinsa ya maye gurbinsa a shugabancin ƙaramar hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta taɓo batun cafke shugaban ƙaramar hukumar Ogbaru, Franklin Nwadialo da hukumar FBI ta yi.

Gwamnatin Anambra ta ce ba za ta ce komai ba ko kare zargin da ake yi wa Franklin Nwadialo na damfara.  

Kara karanta wannan

FBI ta cafke sabon shugaban karamar hukuma a Najeriya kan damfarar $3.3m

Gwamnatin Anambra ta nesanta kanta da shugaban karamar hukuma
Gwamnatin Anambra ta ce ba ruwanta da shugaban karamar hukuma da aka cafke a Amurka Hoto: Res, Roijoy
Asali: Getty Images

FBI ta cafke shugaban ƙaramar hukuma a Anambra

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Law Mefor, ya bayyana hakan ga jaridar The Nation a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar FBI ta kama Franklin Nwadialo a jihar Texas ta Amurka, bisa zarginsa da laifin yin zamba da damfara wacce ta kai dala miliyan 3.3.

Idan har hukumomin Amurka suka tabbatar da zargin, za a iya daure sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar na Anambra har na tsawon shekara 20.

Wataƙila nan ba da jimawa ba za a rantsar da mataimakinsa domin ya zama shugaban ƙaramar hukumar Ogbaru, kamar yadda ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APGA ya bayyana.

Me gwamnati ta ce kan cafke ciyaman a Amurka?

"Mutanensa ne suka zaɓe shi da kuma jam’iyyar siyasar da ya ke. Shi ba wanda Gwamna Soludo ya naɗa muƙami ba ne, don haka ba zan iya magana kan halinsa ba."

Kara karanta wannan

Trump: Bola Tinubu ya taya sabon shugaban ƙasar Amurka murnar lashe zaɓe

"Waɗanda suka zaɓe shi ya kamata su amsa irin waɗannan tambayoyi ko laifin gaskiya ne ko a'a saboda da yawun gwamnatin jiha kawai nake magana ba ƙaramar hukuma ba, cin gashin kai ya zo yanzu."

- Law Mefor

Majiyoyi sun tattaro cewa Gwamna Chukwuma Soludo bai ji daɗin abin da ya faru ba.

Gwamnati ta amince da albashin N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar nan take.

Gwamna Soludo ya bayyana cewa ma’aikaci mafi karancin albashi a jihar Anambra zai samu abin da bai gaza N70,000 ba, duk da cewa zai iya zama tsakanin N78,000 zuwa N84,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng