Jiragen Yakin Sojojin Sama Sun Soye 'Yan Ta'addan ISWAP Masu Yawa a Borno

Jiragen Yakin Sojojin Sama Sun Soye 'Yan Ta'addan ISWAP Masu Yawa a Borno

  • Dakarun sojojin saman Najeriya sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Jami'an tsaron na rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'addan ne a ƙaramar hukumar Marte da ke jihar
  • A yayin hare-haren da sojojin suka kai a ranar, 6 ga watan Nuwamba an sheƙe ƴan ta'addan ISWAP sama da 70

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'addan ISWAP.

Dakarun sojojin sun kai hare-haren ne a kudancin tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta'adda masu yawa.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP a Borpo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun tunkari mayakan sabuwar ƙungiyar ƴan ta'adda, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka hallaka ƴan ta'addan ISWAP

Zagazola Makama ya ce majiyoyi sun bayyana cewa harin da aka kai a ranar 6 ga watan Nuwamba ya mayar da hankali ne kan sansanonin da kwamandan ISWAP, Usman Rasha ke jagoranta.

Ya ce an kai hare-haren ne a tsibirin Kwallaram da Arainna Ciki da ke kusa da Jibilarram a ƙaramar hukumar Marte.

Wata majiya mai tushe da ta ba da rahoton ɓarnar da harin ya yi ta ce an yi nasara sosai, inda ta tabbatar da cewa an kashe mayaƙan ISWAP sama da 70 a sansanin Kwallaram.

Majiyar ta ce yayin da har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a Arainna Ciki ba, amma alamu sun nuna cewa an kashe ƴan ta'adda da dama a yayin harin.

Wannan harin dai na ɗaya daga cikin hare-haren da aka samu nasara sosai wanda jiragen yaƙi na rundunar Operation Hadin Kai suka kai.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun samu babbar nasara, sun kashe ƴan bindiga sama da 400

Sojoji sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojin saman Nigeriya ta samu gagarumar nasara kan yan ta'addan kungiyar Boko Haram.

Sojojin sun kashe yan Boko Haram da dama yayin da suka kai musu wani hari ta jirgin sama suna wani taro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng