Mafi Karancin Albashi: Jerin Jihohin da ba Su Fara Biyan Ma'aikata N70,000 ba
- Ba duka ma’aikatan gwamnati ba ne a jihohi 36 na Najeriya suka fara karɓar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba
- Aƙalla jihohi bakwai da babban birnin tarayya Abuja sun gaza amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata
- Jihohin da suka kasa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi sun haɗa da Zamfara, Sokoto, Osun, Cross River, Imo, Plateau, Taraba, da FCT Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Biyo bayan amincewar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a Najeriya, har yanzu wasu gwamnonin ba su aiwatar da shi a jihohinsu ba.
Aƙalla jihohi bakwai da babban birnin tarayya Abuja sun gaza amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
A cewar jaridar The Punch, jihohin da har yanzu ba su amince da sabon mafi ƙarancin albashi ba, sun haɗa da Zamfara, Sokoto, Osun, Cross River, Imo, Plateau, Taraba, da babban birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikata za su yi jira a Zamfara
Akwai yiwuwar ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara za su jira tsawon lokaci yayin da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal bai daɗe da fara biyan tsohon mafi ƙarancin albashi na N30,000 ba.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, shi ma yana cikin jerin gwamnonin da suka ƙi amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi.
Ba batun mafi ƙarancin albashi a Sokoto da Osun
Bayan da ya yi alƙawura da dama, Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto bai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba.
Lamarin dai haka yake a jihar Osun, inda Gwamna Ademola Adeleke shi ma har yanzu bai amince da wani adadi ko fara biyan mafi ƙarancin albashi ba.
Gwamnan Cross Rivers na biyan N40,000
Gwamna Bassey Otu na jihar Cross shi ma ya gaza aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
A halin yanzu ma’aikatan gwamnati a jihar Cross suna karɓar mafi ƙarancin albashi na N40,000 bayan Gwamna Otu ya amince da shi a ranar 1 ga watan Mayu, 2024, kafin amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Taraba, Plateau da Abuja sun yi shiru
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya ce a shirye ya ke ya biya sabon mafi ƙarancin albashi amma ya kasa farawa bayan ya bayyana hakan a ranar 5 ga watan Satumba.
A jihar Plateau ma ba ta canza zani ba, inda Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang har yanzu bai fara biyan N70,000 ga ma’aikatan gwamnati ba.
Har yanzu ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, bai ce uffan ba kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ga ma'aikata ba.
Ma'aikata sun fara samun N70,000 a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa malaman makarantun firamare a jihar Borno sun fara karbar mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Dubban malaman makarantun firamare a jihar sun yi murna a ranar Juma’a yayin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Asali: Legit.ng