Ana Murna, Malaman Makaranta Sun Fara Karbar Sabon Albashin N70,000 a Jihar Arewa
- Gwamnatin jihar Borno ta fara biyan malaman makarantun firamare sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
- Malaman makaranta da dama sun nuna farin cikinsu yayin kuɗaɗen suka sauka a cikin asusunsu a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamban 2024
- Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Borno ta yabawa Gwamna Babagana Umara Zulum kan fara biyan kudaɗen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Malaman makarantun firamare a jihar Borno sun fara karbar mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Dubban malaman makarantun firamare a jihar sun yi murna a ranar Juma’a yayin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Malaman makaranta sun samu sabon albashi
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa sabon albashin ya shiga asusun malaman ne a ranar Alhamis, mako guda bayan da ma’aikatan gwamnati a jihar suka samu mafi karancin albashin su na watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malaman makaranta da yawa sun sanya hotunan alat na biyan kuɗin a shafukan sada zumunta domin nuna farin cikinsu.
Tun da farko Gwamna Zulum ya sanar da ƙarin albashin ne a ranar 10 ga watan Oktoba a wata ganawa da ya yi da kwamitin aiwatar da mafi ƙarancin albashi.
Gwamnan ya kuma amince da fitar da N3bn domin biyan haƙƙokin iyalan ma’aikatan da suka rasu.
NLC ta yabawa Gwamna Zulum
Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), reshen jihar Borno, ta yaba da mafi ƙarancin albashin jihar a matsayin mafi girma a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban NLC, Kwamared Inuwa Yusuf, ya yabawa Gwamna Zulum, yana mai cewa:
"Mambobin mu sun nuna godiyarsu. Yanzu dai Borno ce ke kan gaba a yankin Arewa maso Gabas wajen biyan albashi, kuma muna yabawa mai girma gwamna bisa wannan nasarar."
Uba Sani ya amince da albashin N72,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.
Gwamna Uba Sani ya amince da N72,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar Kaduna daga watan Nuwamba 2024.
Asali: Legit.ng