Sheikh Dutsen Tanshi: Darasin da Tinubu Zai Koya daga Nasarar Donald Trump a Amurka

Sheikh Dutsen Tanshi: Darasin da Tinubu Zai Koya daga Nasarar Donald Trump a Amurka

  • Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi tsokaci game da zaben kasar Amurka da aka gudanar a farkon makon nan
  • Malamin addinin musuluncin ya na ganin nasarar Donald Trump tattare da ke da darusa ga talakawa da 'yan siyasa
  • Idan Bola Tinubu ya cigaba da watsi da koken talaka, Sheikh Dutsen Tanshi yana yi masa tsoron makomar Joe Biden

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya gabatar da hudubar Juma’a a masallacinsa da ke jihar Bauchi a ranar 8 ga watan Nuwamba.

A hudubar da ya yi, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya tabo batutuwa da-dama, daga ciki akwai zaben shugaban Amurka da aka yi.

Donald Trump
Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya yi magana kan zaben Donald Trump Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Joe Biden ya bukaci Dangote ya dawo da litar man fetur N150?

Kamar yadda aka ji shi ya na bayani a bidiyon hudubar Juma’a da ya wallafa a Facebook, malamin musulunci ya tabo siyasar Amurka.

Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya nuna farin cikinsa game da nasarar Donald J. Trump a kan Kamala Harris da ta yi takara a jam’iyya mai-mulki.

Malamin musuluncin ya bayyana cewa ba komai ya sa shi fatan Trump ya yi nasara ba sai kishin maganar Manzon Allah, Muhammad SAW.

Dutsen Tanshi ya ce Annabi SAW ya fada cewa duk al’ummar da ta damka jagorancinta a hannun mace, ba za ta taba yin nasara ba.

Ganin wasu za su ce ai Amurka ba kasar Musulmai ba ce, malamin ya ce Annabi Muhammad SAW ya yi maganar ne a kan daular Farisa.

"Duk wadanda suka nada mace, sun sabawa Manzon Allah SAW, ko Musulmai ne ko kafirai ne.
"Mu kuma mu na kishin Manzon Allah. Kuma nasarar macen ba daurewa mata gindi ba ne su fito su nema, su sabawa Manzon Allah."

Kara karanta wannan

'Akwai Kwankwaso': Omokri ya jero kusoshi a siyasar Najeriya da suka kayar da Atiku a 2023

- Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

Malam ya ji dadi Trump ya doke Harris

Fitaccen malamin ya soki yadda wasu ‘yan gwagwarmaya su ke amfani da wannan dama, su na kokarin ganin mace ta samu shugabanci.

Malamin ya na tsoron idan da Kamala Harris ta samu nasara, wannan zai taimakawa masu rajin ganin mace ta yi mulki a Najeriya.

Darusan da za a dauka daga Donald Trump

Dr. Dutsen Tanshi ya kawo darasin da za a dauka daga nasarar Trump wanda yake cewa ya fi zama baki-baki a kan abokiyar takarar tasa.

Daga cikin darusun shi ne yadda shugaba Trump ya jajirce wajen komawa mulki duk da tsigewa, rasa zabe, yunkurin kisa da sauransu.

Izinar Tinubu daga zaben kasar Amurka

Sannan ya ce ‘yan siyasa za su dauki izna daga nasarar jam’iyyar Republican ganin yadda gwamnatin Joe Biden ta yi watsi da talakawa.

Shehin ya ce Biden ya gaza shawo kan matsalar tattalin arziki, tsadar rayuwa, rikicin Gaza, batun auren jinsi don haka aka yi waje da su.

Kara karanta wannan

Trump Vs Harris: Malamin addini ya hango abin da ke shirin faruwa a zaben Amurka

Idan Bola Tinubu bai saurari koken jama’a na cire tallafin mai da kuncin rayuwa ba, malamin ya na ganin hakan na iya faruwa a 2027.

Donald Trump ya fara shirin hawa mulki

A ranar Juma'a labari ya zo cewa zababben shugaban Amurka, Donald Trump ya yi nadin farko makonni kafin ya kafa gwamnatinsa.

Donald Trump ya nada Susie Wiles a matsayin shugabar ma'aikatan fadar White House bayan ta jagoranci yakin neman zabensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng