An Kashe Mutum yayin Kona Gidan 'Dan Siyasa, Yan Sanda Sun Fara Bincike
- Wasu da ake zargin yan kungiyar asiri ne sun kai farmaki gidan tsohon kansila a jihar Ribas, amma ba su same shi a gida ba
- Sai dai matasan dauke da manyan bindigu sun hallaka mutum guda yayin da su ka illata wasu mutane guda hudu yayin harin
- Tsohon kansila da aka kai harin gidansa, Chigozie Wok ya zargi wani shugaban kungiyar asiri da ake kira ‘Naked’ da kai harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Wasu miyagun mutane sun hallaka dan kungiyar bijilanti da ke jihar Ribas a daidai lokacin da su ke bankawa gidan tsohon kansila a yankin wuta.
Lamarin ya afku a karamar hukumar Emohua da ke jihar Ribas inda aka kai hari gidan tsohon Kansila tare da kashe jami’in tsaron sa kai na kungiyar zaman lafiya ta Ogba-Egbema-Ndoni .
Jaridar Punch ta wallafa cewa ana zargin wadanda su ka kai harin yan kungiyar asiri ne, kuma sun raunata mutane akalla guda hudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kona gidan tsohon jami’in gwamnatin Ribas
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ana zargin wasu matasa yan kungiyar asiri sun kai hari, suka rika harbe harbe a gidan tsohon kansila, Chigozie Wok a jihar Ribas.
Daya daga cikin wadanda su ka tsira daga harin da ya bayyana sunansa da Eze ya ce su na zaune a gida sai su ka fara jin karar harbe-harbe, yayin da wasu su ka tunkaro inda su ke bisa zargin hada kai da yan sanda.
"An yi mani barazana:" Tsohon kansilan Ribas
Tsohon kansila, Chigozie Woka dan asalin yankin Obele, ya zargi wani jagoran yan kungiyar asiri da ake kira ‘Naked’ da kitsa harin da ya salwantar da ran mutum guda bisa zargin aiki da yan sanda.
A jawabinta, kakakin rundunar yan sandan Ribas, Grace Iring Koko ta tabbatar da kai harin, inda ta yi baynin cewa ana zurfafa bincike.
An kai hari jihar Ribas
A baya mun ruwaito cewa wasu maharan sun kai hari sansanin Quarry da ke karamar hukumar Akamkpa a jihar Ribas tare da salwantar da ran babban jami'in dan sanda.
Rundunar yan sandan jihar ta bakin kakakinta a jihar Ribas, SP Nelson Okpabi ta tabbatar da harin da aka kai a ranar Alhamis, 7 Nuwamba, 2024 kuma har an sace wasu yan kasar China.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng